Masu Garkuwa da mutane sun kashe Dan Kungiyar kwadago ta Kasa NLC.
Kungiyar kwadago ta kasa NLC tayi Rashin Babban Member dinta Comrade Lawal MG.
Wannan na zuwa ne kuwa bayan da masu garkuwa da Mutane suka yi garkuwa dashi a watannin da suka gabata.
Anyi garkuwa da Marigayi Lawal MG ne da wasu mutanen lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Birinin tarayya Abuja a watanni uku zuwa hudu da suka gabata.
Lawal MG dai Mazaunin Garin Mahuta ne a gundumar Afaka dake karamar hukumar Igabi ta jihar kaduna.
Bincike Sun nuna cewa a jiya talata ne aka tabbatar da cewa yan bindigan sun kasheshi bayan kai musu makudan kudaden da suka bukata.
Kani ga mamacin, Isah Musa Zuru Shine ya tabbatar da mutuwar yayan nasu a kafar sada zumuntarsa na Facebook da kuma whatapp.
Allah ya gafarta masa ya kuma kai haske kabarinsa ya baiwa iyalansa da sairan yan uwa hakurin jure raahinsa.
Kafin Rasuwarsa Comrade Lawal MG ma'aikaci ne a Babban Asibitin Ido na kasa dake Nan kaduna.
Matsalar Rashin tsaro dai na ci gaba da ciwa alummar Najeriya kasa a gwiwa wanda akwai bukatar Gwamnati ta mike tsaye wajen kawo karshen matsalar.
Usman Ibrahim.


Comments
Post a Comment