Posts

Showing posts with the label Labaran Wasanni

Kasu zata kece Raini da ATBU Bauchi a gasar Manyan Makarantu ta kasa

Image
A ranar Laraba mai zuwa ne Kungiyar kwallon kafa ta Daliban Jami'ar kaduna zata kece Raini da kungiyar kwallon kafa ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi wato ATBU a gasar Manyan makarantu ta kasa wato NiFL.  A zantawar da wakilin labaran Mahuta Newspaper yayi da Sakataren shirya wasanni na jami'ar jihar kaduna, Malam Dahiru Musa ya bayyana cewa fatan su a wasan shine su samu nasara a sahun farko a wasan kafin zuwa sahu na biyu.  Malam Dahiru ya kara da cewa wannan shine karan farko da kasu ke fafatawa a gasar kuma fatanta shine ta lashe gasar a karan farko. Ya kuma bukaci dukkan yan wasan da masu horas dasu da su zage Damtse don ganin sun samu nasara a wasan da zai gudana a ranar laraba mai zuwa 3 ga watan Ogustan 2022. A nashi bangaren Kocin kungiyar da Kasu, Coach Tajidden Delima Saka ya janyo hankalin yan wasansa ne su tabbatar sun jajairce a wasan inda ma yayi kira ga magoya baya da su mara musu baya don cimma nasarar da ake bukata. Wannan wasa dai ana fatan ga...