Posts

Young Spiders ta lashe Gasar cin kofin Zaman Lafiya na Gwamna Uba Sani

Image
Young Spiders Kasuwan Magani ta lashe Gasar cin kofin Zaman Lafiya na Gwamna Uba Sani. Daga Usman Ibrahim  9 ga watan Ogustan, 2026. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Young Spiders ta Kasuwan Magani ta zama zakarar gasar cin kofin kwallon kafa na Gwamnan Uba Sani  da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, bayan da ta doke Kufana United da ci 2–0 a wasan ƙarshe. An gudanar da wasan ƙarshen ne a filin wasa na Kajuru Township Stadium, inda dimbin masoya ƙwallon ƙafa, shugabannin al'umma, jami'an gwamnati da sauran manyan baƙi daga ciki da wajen ƙaramar hukumar suka halarta. Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Muhammad Shuaibu, ne ya shirya gasar da nufin inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummomi daban-daban na yankin, tare da nuna goyon baya ga gwamnatin Gwamna Uba Sani.    Young Spiders ce ta fara samun damar cin ƙwallo, inda Sagiru Gambo ya buɗe ƙwallon a minti na 12, bayan da ya samu damar zura ƙwallon a raga. Ana tsaka da wasa...

Hon. Dauda Madaki ya Jaddada Aniyar Gwamnatin sa wajen Inganta tsarin Shugabanci ta hanyar anfani da Sahihan Bayanai.

Image
  HON. DAUDA MADAKI YA JADDADA ANIYAR GWAMNATINSA NA INGANTA TSARIN SHUGABANCI TA HANYAR AMFANI DA SAHIHAN BAYANAI. Daga, Usman Ibrahim Mahuta. 5 ga watan Ogustan, 2026. Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Kajuru, Honorable Dauda Madaki ya bayyana cewa gwamnatin sa zata ci gaba da barin kofarta a bude wajen gudanar da harkokin Shugabanci ga Al'umma don ci gaba. Dauda Madaki ya bayyana haka ne a cikin wata Sanarwa data samu Sanya hannun Sakataren yada labaran sa, Mr. John Ezra Sojah. Hukumar kula da kasafi da tsare-tsare ta Jihar kaduna tare da hadin gwiwar Hukumar UNICEF Ofishin kaduna ne suka shirya taron karawar Juna sanin na kwanaki Uku ga Shugabannin kananan Hukumomin Jihar kaduna a taron daya gudana a Jihar Kano. A cewar Sanarwar, Dauda Madaki ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin sa na ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Kaduna da UNICEF da sauran abokan hulɗar domin ƙarfafa ƙwarewar hukumomi, bunƙasa shugabanci mai haɗa kowa da kowa, da aiwatar da shirye-shiryen da za su...

Allah ya yiwa Sheik Shehu Usman Rigi-Rigi rasuwa

Image
2 ga Janairu, 2026 Labari daga Abubakar Dan Yaro Innalillahi wainnailaihirrajiun: Allah ya yiwa Fitacccen Malamin Addinin Musulunci nan a Jihar Kaduna, Sheik Shehu Usman Idriss wanda aka fi Sani da Regi-regi na Manzon Allah. Kafin rasuwarsa Malamin ya shahara Wajen sanya mabiyansa da Sauran Al'ummar Musulmai nishadi Saboda salon wa'azinsa. Shiek Shehu Usman ya rasu ya bar Matansa 4 da yara 37 da jikoki da dama  Za'a gudanar da Jana'izarsa da Karfe 4:30pm na yammacin yau idan Allah ya kaimu a Gidansa dake Kusfa Zaria. Da Fatan Allah ya gafarta Masa da Rahama Amin.

Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.

Image
  Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi. 2 ga Janairu, 2026 Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta samu wata gagarumar nasara a yaƙin da take yi da satar mutane da fashin daji, inda ta ceto mutane biyu da aka sace tare da cafke wani wanda ake zargi, a yayin wasu aikin hadin gwiwa na magance matsalar tsaro da aka gudanar a ƙananan hukumomin Kalgo da Dandi na jihar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce aikin ya nuna ƙudirin rundunar na hana masu aikata laifuka samun mafaka a cikin jihar. Usman ya ce an ceto mutanen ba tare da sun ji rauni ba, sakamakon daukin gaggawa da jami’an tsaro da kuma kyakkyawar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Sa-kai ta Vigilante Group suka yi. Ya sake jaddada ƙudirin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi na amfani da bayanan sirri da kuma ɗaukar matakan kariya tun kafin aikata laifi, yana mai tabbatar wa al’umma cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka do...

Rundunar sojin Najeriya ta kashe mataimakin shugaban Boko Haram a Jihar Borno

Image
  Rundunar soji ta kashe mataimakin shugaban Boko Haram   2 ga Janairu, 2026 Daga Usman Ibrahim   Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe wani babban jagoran Boko Haram, wanda aka bayyana shi a matsayin mataimaki na biyu tare da wasu mayaka goma a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno. An bada rahoton cewa an kashe ‘yan ta’addan ne a yankin Komala da ke Ƙaramar Hukumar Konduga yayin wani samame da rundunar ta kai da daddare. A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sanni Uba ya fitar, ta ce an kuma kwato makamai da dama daga hannun yan ta’addan. Ya ce lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan da sojoji suka hallaka fitaccen kwamandan Boko Haram da ISWAP, Julaibib a yankin Gujba na Timbuktu Triangle. Ya ƙara da cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar da harsasai da kekuna da kayayyakin abinci da kuma magunguna masu yawan gaske. Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka. Facebook YCMC News You Tube YCMC News Tit Tok YCMC New...

Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.

Image
  Besiktas taki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi. 2 ga Janairu, 2026 Daga Usman Ibrahim. kyakkyawan salon wasa da ɗan wasan tsakiya Wilfred Ndidi ya nuna a matakin kungiyarsa da ƙasarsa Najeriya ya ja hankalin ƙungiyar kwallon kafa ta Ajax dake   kasar Netherlands sai dai ƙungiyar Beşiktaş ta ƙi amincewa da tayin da aka kawo mata. Rahotanni sun nuna cewa tayin da aka tattauna ya ƙunshi aro na Yuro Miliyan Biyu ( €2m) tare da zaɓin saye na Yuro Miliyan ( €12m ) amma Beşiktaş ba ta shirya karɓar wannan tayin a wannan lokaci ba. Ndidi ya taka muhimmiyar rawa a tsakiya tare da baiwa tawagar Super Eagles gagarumin gudunmuwa a gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afirika wato AFCON na 2025 da aka kammala a kasar Morocco inda Najeriya ta kammala gasar a matsayi na uku tare da lashe lambar tagulla. Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka. Facebook YCMC News You Tube YCMC News Tit Tok YCMC News

Dan wasan Najeriya Gabriel Orok ya sanya hannu a kungiyar Al Swehli ta Kasar Libya daga Emyimba FC.

Image
  Gabriel Orok ya sanya hannu a kungiyar Al Swehli ta Kasar Libya daga Emyimba FC.   2 ga Janairu, 2026 Daga Usman Ibrahim. Dan wasan gefe na Najeriya Gabriel Orok ya kammala komawarsa dindindin zuwa ƙungiyar Al Swehli ta ƙasar Libya. Gabriel ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku da ƙungiyar ta Arewacin Afirka. Tsohon ɗan wasan Enyimba FC ya kammala sauya shekan ne bayan ya yi nasarar gwajin lafiya tare da cimma matsaya kan sharuɗɗan kwantaragin da kulob ɗin. Al Swehli ta riga ta gabatar da Orok a hukumance, tana mai tabbatar da isowarsa gabanin kakar wasa mai zuwa. Sauyin da Orok ya yi alama ce ta buɗe sabon babi a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, kasancewar wannan ne karon farko da zai taka leda a Arewacin Afirka. Ana sa ran ƙwarewarsa ta gudu, kai hari kai tsaye da iya kutsa kai za su ƙara wa sabuwar kungiyarsa Al Swehli ƙarfi a ɓangaren gefe wajen rika kai kora. Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka. Facebook YCMC News You Tube YCMC News Tit...