Kasu zata kece Raini da ATBU Bauchi a gasar Manyan Makarantu ta kasa



A ranar Laraba mai zuwa ne Kungiyar kwallon kafa ta Daliban Jami'ar kaduna zata kece Raini da kungiyar kwallon kafa ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi wato ATBU a gasar Manyan makarantu ta kasa wato NiFL.

 A zantawar da wakilin labaran Mahuta Newspaper yayi da Sakataren shirya wasanni na jami'ar jihar kaduna, Malam Dahiru Musa ya bayyana cewa fatan su a wasan shine su samu nasara a sahun farko a wasan kafin zuwa sahu na biyu.

 Malam Dahiru ya kara da cewa wannan shine karan farko da kasu ke fafatawa a gasar kuma fatanta shine ta lashe gasar a karan farko.

Ya kuma bukaci dukkan yan wasan da masu horas dasu da su zage Damtse don ganin sun samu nasara a wasan da zai gudana a ranar laraba mai zuwa 3 ga watan Ogustan 2022.

A nashi bangaren Kocin kungiyar da Kasu, Coach Tajidden Delima Saka ya janyo hankalin yan wasansa ne su tabbatar sun jajairce a wasan inda ma yayi kira ga magoya baya da su mara musu baya don cimma nasarar da ake bukata.

Wannan wasa dai ana fatan ganin cewa zai gudana cikin nasara a Shalkwatar Jami'ar dake nan kaduna.

A ranar 17 ga watan Ogusta ne kungiyar zata ziyarci Jami'ar ta ATBU domin fafatawa a wasan sahu na biyu domin sanin wanda zai samu nasara zuwa zagaye na gaba.


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma