Posts

Showing posts from February, 2024

Gwamna Zulum ya baiwa Manoma Tallafi a Damasak.

Image
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar  Borno yayi alkawarin rage irin radadi na halin da alumma musanman manoma suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur a Damasak shalkwatar karamar hukumar Mobbar ta jihar domin bunkasa tsarin samar da wadataccen Abinci a jihar. Garin Damasak, daya ne daga cikin yankunan da jihar Borno ke alfahari dashi wajen samar da abinci, yankin sannu a hankali yana farfadowa bayan kwashe tsawon shekaru Suna cikin matsala sakamakon Rikicin kungiyar Boko Haram. Gwamnan na magana ne lokacin da yake ziyarar aiki na kwana biyu domin duba yadda ake raba kayan tallafi ga matan da suka rasa mazajen su da mata masu karamin karfi, ya kuma yi Alkawarin maida jihar Borno cikin jihohin da suka fita daga duk wata matsala ta karancin abinci a kasarnan. Ya kuma sha alwashin basu gudunmuwar Injin ban ruwa mai anfani da hasken Rana da iri na shuka da takin zamani a dai sauran kayayyakin aikin gona don ci gaban jihar. Daga Abubakar Abdullahi. Labaran YCMC media Kaduna.

Gamayyar kungiyoyin Arewa Sun koka akan tsadar kayan Masarufi

Image
  Talata 6-2-2024 7:00pm Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun bayyana damuwarsu akan yadda kayayyakin masarufi ke ci gaba da tashin gwauron zabi a fadin Kasarnan. Jaridar Daily Trust ta bada Rahoton cewa,  yan Najeriya daban daban suna ci gaba da nuna Damuwa da fargaba a sakamakon halin kunci da suke ciki sakamakon hauhawar farashin kayayyaki. Kamar su Shinkafa da Filawa da Siga da Siminti da dai sauransu kuma an danganta lamarin akan yadda farashin Naira ke ci gaba da faduwa a kasuwan cinikayyar kudi wanda hakan yasa alumma basa iya rayuwa cikin Natsuwa da wadata. A cikin wata Sanararwa da Shugaban Gamayyar kungiyar na kasa , Jamilu Aliyu Charanchi, ya fitar ya ce  lamarin ya kai yan Najeriya ga Bango matuka wanda ke bukatar a dauki kwararan matakai da suka da ce. Labaran YCMC media Kaduna.

Anyi Kiran Sanya Dokar ta Baci a bangaren Abinci a Najeriya

Image
Talata 6-2-2024. 7:00pm Kungiyar yan jarida masu rajin tabbatar da Zaman lafiya a jihar kaduna (NPJK) ta bukaci a Sanya dokar ta baci a bangaren samar da issshen abinci a fadin kasarnan. Ta Bukaci Gwamnatin tarayya Dana jihohi su dauki kwararan matakan da suka dace don saukakawa alumma halin kunci da suke ciki yanzu haka na matsin Rayuwa. Mallam Ibrahim Yakubu, shine Shugaban tawagar ta NPJK, ya bayyna wasu dalilai daya sa alumma suke fama da wahala musanman Mata da kananan yara wanda ya hada da tashin farashin man fetur da cire tallafin mai wanda ke matukar yin illa ga rayuwar yan Najeriya. Yayi kira da a dauki matakan da suka dace don kawo mafita ga wannan hali da ake ciki, yayin da ya bukaci Gwamnatocin jihohi su tattauna da Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu don sanya dokar ta baci a bangaren samar da binci isasshe a Najeriya. Labaran YCMC media Kaduna.

Abubakar Signed five year deal with F c Gent of Belgium

Image
Nigeria's Golden Eaglets striker Abubakar Abdullahi Idris has signed a four and half year contract with Belgium Club side F c Gent. A top source From his Manager, revealed that the youngster, who made a name for himself with his brace in the final of the WAFU B AFCON qualifying tournament in Ghana is expected to make another name in Belgium. The Kaduna based Footballer, Abubakar Abdullahi who joined Gent from Jega United of Kebbi State Nigeria, has perform well in the club program before his signing  with the Belgium Club side. Speaking after the signing, Abubakar thanked his parents, guidance and his Managers and those that supported him towards his success and urged them to continue to pray for him. YCMC MEDIA.