Gwamna Zulum ya baiwa Manoma Tallafi a Damasak.



Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar  Borno yayi alkawarin rage irin radadi na halin da alumma musanman manoma suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur a Damasak shalkwatar karamar hukumar Mobbar ta jihar domin bunkasa tsarin samar da wadataccen Abinci a jihar.

Garin Damasak, daya ne daga cikin yankunan da jihar Borno ke alfahari dashi wajen samar da abinci, yankin sannu a hankali yana farfadowa bayan kwashe tsawon shekaru Suna cikin matsala sakamakon Rikicin kungiyar Boko Haram.

Gwamnan na magana ne lokacin da yake ziyarar aiki na kwana biyu domin duba yadda ake raba kayan tallafi ga matan da suka rasa mazajen su da mata masu karamin karfi, ya kuma yi Alkawarin maida jihar Borno cikin jihohin da suka fita daga duk wata matsala ta karancin abinci a kasarnan.

Ya kuma sha alwashin basu gudunmuwar Injin ban ruwa mai anfani da hasken Rana da iri na shuka da takin zamani a dai sauran kayayyakin aikin gona don ci gaban jihar.


Daga Abubakar Abdullahi.


Labaran YCMC media Kaduna.

Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma