Gamayyar kungiyoyin Arewa Sun koka akan tsadar kayan Masarufi

 


Talata 6-2-2024 7:00pm

Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun bayyana damuwarsu akan yadda kayayyakin masarufi ke ci gaba da tashin gwauron zabi a fadin Kasarnan.

Jaridar Daily Trust ta bada Rahoton cewa,  yan Najeriya daban daban suna ci gaba da nuna Damuwa da fargaba a sakamakon halin kunci da suke ciki sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Kamar su Shinkafa da Filawa da Siga da Siminti da dai sauransu kuma an danganta lamarin akan yadda farashin Naira ke ci gaba da faduwa a kasuwan cinikayyar kudi wanda hakan yasa alumma basa iya rayuwa cikin Natsuwa da wadata.

A cikin wata Sanararwa da Shugaban Gamayyar kungiyar na kasa , Jamilu Aliyu Charanchi, ya fitar ya ce  lamarin ya kai yan Najeriya ga Bango matuka wanda ke bukatar a dauki kwararan matakai da suka da ce.


Labaran YCMC media Kaduna.


Comments