Anyi Kiran Sanya Dokar ta Baci a bangaren Abinci a Najeriya



Talata 6-2-2024. 7:00pm

Kungiyar yan jarida masu rajin tabbatar da Zaman lafiya a jihar kaduna (NPJK) ta bukaci a Sanya dokar ta baci a bangaren samar da issshen abinci a fadin kasarnan.

Ta Bukaci Gwamnatin tarayya Dana jihohi su dauki kwararan matakan da suka dace don saukakawa alumma halin kunci da suke ciki yanzu haka na matsin Rayuwa.

Mallam Ibrahim Yakubu, shine Shugaban tawagar ta NPJK, ya bayyna wasu dalilai daya sa alumma suke fama da wahala musanman Mata da kananan yara wanda ya hada da tashin farashin man fetur da cire tallafin mai wanda ke matukar yin illa ga rayuwar yan Najeriya.

Yayi kira da a dauki matakan da suka dace don kawo mafita ga wannan hali da ake ciki, yayin da ya bukaci Gwamnatocin jihohi su tattauna da Shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu don sanya dokar ta baci a bangaren samar da binci isasshe a Najeriya.


Labaran YCMC media Kaduna.

Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma