Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.


 

Besiktas taki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.

2 ga Janairu, 2026

Daga Usman Ibrahim.

kyakkyawan salon wasa da ɗan wasan tsakiya Wilfred Ndidi ya nuna a matakin kungiyarsa da ƙasarsa Najeriya ya ja hankalin ƙungiyar kwallon kafa ta Ajax dake  kasar Netherlands sai dai ƙungiyar Beşiktaş ta ƙi amincewa da tayin da aka kawo mata.

Rahotanni sun nuna cewa tayin da aka tattauna ya ƙunshi aro na Yuro Miliyan Biyu (€2m) tare da zaɓin saye na Yuro Miliyan (€12m) amma Beşiktaş ba ta shirya karɓar wannan tayin a wannan lokaci ba.

Ndidi ya taka muhimmiyar rawa a tsakiya tare da baiwa tawagar Super Eagles gagarumin gudunmuwa a gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afirika wato AFCON na 2025 da aka kammala a kasar Morocco inda Najeriya ta kammala gasar a matsayi na uku tare da lashe lambar tagulla.

Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka.

Facebook YCMC News

You Tube YCMC News

Tit Tok YCMC News


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.