Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

 

Polytechnic


Daga Auwal Ahmed Ibrahim, Goronyo.

31 ga Janairu 2026

Hukumar Gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya dake Jihar Kaduna (Kadpoly) ta fitar da sanarwa domin amsa korafe-korafen da wasu daliban da suka kammala karatu ke yi game da jinkirin kiran su aikin bautar ƙasa ta NYSC.

Hukumar ta bayyana cewa wannan jinkiri ba na Kadpoly kaɗai ba ne, illa ya shafi dukkan manyan makarantu a faɗin ƙasar nan, musamman waɗanda ke da yawan ɗaliban da suka kammala karatu, sakamakon yawan tantance bayanai da matakan da ake bi.

A cikin Sanarwa ta Musamman da Magatakardar Kwalejin, Dr. Muhammad Tanimu, ya rubuta kuma ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa manyan abubuwan da ke haddasa jinkirin sun haɗa da rashin yin daidaitaccen regularization da Hukumar Shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Ƙasa JAMB), kura-kurai ko rashin cika takardun da ake buƙata daga ɓangaren waɗanda suka kammala karatu, da kuma tsarin rukunnan dalibai wato batch da NYSC ke amfani da shi.

Magatakardar ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin shirya tura waɗanda suka kammala karatu a shekarar 2024 cikin rukuni-rukuni na gaba, yayin da waɗanda suka kammala a shekarun baya amma har yanzu ba a tura su ba, aka shawarce su da su je wurin Jami’in NYSC na makarantar domin samun shawarwari da jagora.

Hukumar Gudanarwa ta jaddada cewa samun yardar (clearance) daga hukumar (NERD) ya zama dole kafin a ci gaba da aikin tura masu bautar ƙasa. 

Duk masu shirin zuwa NYSC dole ne su yi rajista da NERD kuma su samu wannan yardar domin kauce wa ƙarin jinkiri.

Hukumar ta roƙi dukkan waɗanda abin ya shafa musamman waɗanda suka kammala karatu da masu shirin zuwa yiwa Kasa hidima da su yi haƙuri a yayin da ake ci gaba da aikin tantancewa da shirye-shiryen tura su, tare da tabbatar da cewa sun cika dukkan abubuwan da suka rataya a wuyansu.

Daga Jaridar Education Vanguard

Comments

Popular posts from this blog

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

Brazil ta Doke Najeriya da ci 1-0