Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.

 



Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.

2 ga Janairu, 2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta samu wata gagarumar nasara a yaƙin da take yi da satar mutane da fashin daji, inda ta ceto mutane biyu da aka sace tare da cafke wani wanda ake zargi, a yayin wasu aikin hadin gwiwa na magance matsalar tsaro da aka gudanar a ƙananan hukumomin Kalgo da Dandi na jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce aikin ya nuna ƙudirin rundunar na hana masu aikata laifuka samun mafaka a cikin jihar.

Usman ya ce an ceto mutanen ba tare da sun ji rauni ba, sakamakon daukin gaggawa da jami’an tsaro da kuma kyakkyawar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Sa-kai ta Vigilante Group suka yi.

Ya sake jaddada ƙudirin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi na amfani da bayanan sirri da kuma ɗaukar matakan kariya tun kafin aikata laifi, yana mai tabbatar wa al’umma cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka domin tarwatsa cibiyoyin masu satar mutane a faɗin jihar.

Rundunar ta kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai akan lokaci, tana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kebbi.

Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka.

Facebook YCMC News

You Tube YCMC News

Tit Tok YCMC News


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.