KASU 0-2 ATBU BAUCHI

 



A yau ne aka gurza kwallo tare da kece raini tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kasu da ATBU bauchi a wasan sahun farko na manyan makarantu.

Wasan dai bai yiwa alummar jihar kaduna dadi ba sakamakon yadda tawagar daliban kasu suka yi rashin nasara a hannun tawagar Bauchi Da ci 2-0.

Dan wasan ATBU ya fara zura kwallo a cikin minti 8 na wasan bayan da magoya bayan kasu suka yi ihu inda suke zargin dan wasan yayi satan fage amma alkalin wasa ya ce wannan kwallo ta halasta inda wasa ya kasance daya da nema.

Jim kadan a kammala wasan ne, tawagar ta Bauchi ta kara samun daman zura kwallo na biyu a wasan a dai dai lokacin da tawagar Kasu ke kokarin rama kwallo daya da aka cita amma gakarta ya ci tura.

Da yake jawabi jim kadan bayan kammala wasan, Mai horas da tawagar Kasu Coach Tajudden Delima Saka ya yabawa daukacin yan wasansa bisa yadda suka taka leda yadda ya kamata a wasan.

coach Tajudden yama bayyana cewa zasu ci gaba da kokari tare da shiryawa wasan su sahu na biyubda zasu fafata a ranar 17 ga watan Ogustan wannan shekarar a jihar Bauchi.

A nashi bangaren Sakataren harkokin wasannni na Kasu Malam Dahiru Musa Mahuta ya ce yan wasan sunyi matukar kokari sun kai kora da dama amma kwallo taki shiga Ragar Bauchi, ya kuma bukace su da su sake zage Damtse a wasan sahu na biyu da zasu kara a nan gaba.

Dalibai da malamai sauran masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni ne suka halarci wannan wasan wanda ya dauki hankali masu kallo.

Shima Cocin Bauchi ya bayyana farin cikin sa ne bisa nasarar daya samu a wasan.


Usman Ibrahim Mahuta.


Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma