Dan wasan Kaduna ya Sanya hannu Akan kwantiragin shekara guda


 

Matashin Dan wasa Daga Jihar Kaduna Jibril Muhammad ya Sanya hannu Akan kwantiragin shekara guda Da kungiyar kwallon kafa ta Best talent football Dake jihar Lagos.

Jibril Muhammad Wanda Dan asalin kungiyar kwallon kafa ta Divine football Club ne a Barikin horas Da kananan hafasoshin soji anan Kaduna Yana cikin sabbin Yan Wasa Da wasan Da kungiyar  Best Talent ta Siya a shirye shiryen Fara gasar National league NLO ta kasa.

Dan wasan,Jibril Muhammad kafin Sanya hannunsa a Sabuwar kungiyar  Yana cikin Yan wasan Da suka taimakawa kungiyar kwallon kafa ta DMF Football Academy Dake Mahuta a gasar Ramadan Cup Na 2021 Da Na 2022.

Mai Horas Da kungiyar kwallon kafa ta Divine FC Sulaiman Dari, Wanda akafi Sani Da Coach Rosi ya tabbatar Da Sanya hannu Dan wasan a lokacin zantawarsu Da Wakilin labaran wasannin Ksmc Kuma yayi mishi fatan samun nasara a rayuwarsa.

Jibril Muhammad Mai shekaru 16 Da haihuwa Dan wasan tsakiyar ne Mai taimakawa Yan wasan gaba  Kuma ana Saran Zai Samu isasshen lokacin buga Wasa a Sabuwar kungiyar sa ta  Best talent football Club.


Usman Ibrahim.


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma