Arewa maso yamma ta lallasa kudu maso gabas 7-0 a ci gaba da gasar YSFON U-16 na kasa a kaduna

 



A lahadinnan ne 18 GA Watan yunin 2023  dai tawagar kwallon kafa ta shiyyar arewa maso yamma ta doke tawagar kwallon kafa ta yankin kudu maso gabas da ci bakwai da nima.

Dan wasan shiyyar arewa maso yamma, yahatu Mula wanda ya fito daga jihar kebbi shine ya zura kwallaye har guda 4 inda kuma tsohon dan wasan Njeriya Garba Lawal ya bashi kyautar wanda yafi taka leda a wasa.

Yayin da a wasa na biyu da aka buga tawagar kwallon kafa ta shiyyar arewa ta tsakiya ta lallasa Rivers da ci uku da nima.

Sai kuma a yau litinin za a fafata sauran wasanni takwas na rukuni inda yanzu haka a ke fafata wasa tsakanin kudu maso kudu da kuma arewa maso gabas yayinda har ila yau gudu maso gabas zata kara da arewa ta tsakiya sai arewa ta yamma ta kara bugawa da Rivers yayin da arewa ta tsakiya zata fafata da arewa ta yamma sai wasan rukuni na karshe zai gudana tsakanin Rivers da kudu maso gabas da karfe 3 da kwata.


Usman Ibrahim.








Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma