Dan wasan Flying Eagles Haliru Sarki ya Sanya hannu Da kungiyar Al Ain.
Dan wasan tawagar Flying Eagles ta najeriya Haliru Sarki ya sanya hannu akan kwantiragi da kungiyar kwallon kafa ta Al Ain dake yankin larabawa.
Wannan kuwa na zuwa ne bayan da dan wasan ya nuna bajinta a gasa
r cin kofin duniya na yan kasa da shekaru 20 da aka kammala a kasar Argentina.
Da take tabbatar da sanya hannun kungiyarsa, Mahanaim FC tace tuni suka cimma yarjejeniya dan wasan Haliru Sarki da kungiyar da Al Ain kan daukarsa.
Haliru Sarki, na daya daga cikin yan wasan najeriya da suka taimakawa najeriya ta samun zuwa mataki na gaba a gasar bayan zura kwallaye inda daga bisa Sukai rashin Nasara a hannun Korea.
Usman Ibrahim

Comments
Post a Comment