Najeriya ta Samu Tikitin zuwa gasar Cin kofin kasahsen Nahiyar Afirika Na 2023.
Kwallon karshe da Dan wasan najeriya Kelechi Iheanacho ya zura a wasam da najeriya ta doke Saliyo ne ya baiwa tawagar super eagles daman samun tikitin zuwa gasar cin kofin kasashen nahiyar afirka na 2023 da zai gudana a kasar Ivory Coast.
Dan wasa Victor Osimhen ne ya zura kwallaye biyu a wasan a cikin minti 19 da 32 yayin da dan wasan saliyo Mustapha Bundu ya rama kwallo guda a minti 41 yayin da bayan an dawo hutun rabin lokacin dan wasan saliyo Augustine Kargbo ya maida wasa 2 da 2 inda ana dab da Karkare wasa dan wasan super eagles Kelechi Iheanacho ya zura kwallo ta uku wa najeriya inda najeriya ta doke saliyo da ci uku da biyu.
Yanzu haka Guinea Bissau ta koma ta biyu a teburin rukunin amma kuma itama ta samu tikitin zuwa gasar sau hudu kenan a jere.
Yayin da kuma a wani bangaren, dan wasa Victor Osimhen yasha gaban yan wasa Ahmad Musa da Ighalo a yawan zurawa majeriya kwallo inda yake da 17 yayin da kuma har yanzu marigayi tsohon dan wasan najeriya Rashidi Yekini yasha gaban dukkan yan wasan najeriya wajen cin kwallo inda babu wanda ya zura fiye da nashi guda 35 yayin da Yakubu Aiyegbeni keda 22 sai Obafemi Martins 18 sai Ahmed Musa 16 and Odion Ighalo 15.
Usman ibrahim.

Comments
Post a Comment