Tawagar Arewa maso gabas ta lashe gasar YSFON Na kasa Bayan doke Arewa maso yamma a wasan karshe


 Tawagar kwallon kafa ta YSFON Na shiyyar Arewa Maso gabas ta lashe gasar YSFON U-16 na kasa Da aka kammala a jihar Kaduna Bayan doke shiyyar Arewa Maso yamma daci Daya mai ban haushi a wasan karshe.

Wasan karshen Wanda ya gudana a filin wasa Na Ahmadu Bello Dake nan Kaduna ya Samu halartar manyan baki Da suka fito Daga bangarori daban daban Da sauran yan kallo Da suka fito Domin Shaida gasar na kasa.

Dan wasan Arewa maso gabas Abdulrahman Ali shine ya zura kwallo guda data makale tun kafin aje Hutun Rabin lokaci Na wasan a gaban Yan kallo musanman magoya bayan shiyyar Arewa Maso yamma.

Tawagar Arewa Maso yamma ta rinka matsa lamba wa tawagar Arewa maso gabas Dan ganin ta Rama kwallon Amma kokari Da jajurewa Na mai tsaran raga Na tawagar Arewa maso gabas Adamu Ibrahim yasa an gaza Rama kwallon Kuma tawagar Arewa maso gabas ce ta lashe gasar.

Da yake jawabi Bayan Mika kofin GA Wanda suka lashe, Kwantrola na hukumar shige Da fice ta kasa reshen jihar Kaduna,Bashir Muhammad Lawal ya bayyana Farin cikinsa bisa irin kokari Na daukacin Yan wasan Da suka fafata gasar Sai ya bukace su dasu sake jajurcewa don ganin sun cimma nasara rayuwarsu ta kwallon kafa.

A yayin Da yake yabawa kungiyar YSFON bisa Shirya gasar, Controller ya bayyana cewa hukumar shige Da fice a shirye take Kuma Za tayi Duk mai yuwuwa na ganin ta tallafawa harkokin wasanni a bangarori daban daban musanman ma a matakin karkara.

Shima Da yake jawabi, Daya Daga cikin manyan baki Kuma Wanda ya taba anfana Da Shirya wasanni Da YSFON keyi a lokacin Yana Taka Leda, Mansur Abubakar ya ce akwai dunbin Yan Wasa hazikai a Najeriya Da Idan aka tallafa musu zasu Iya wakiltar Najeriya a gasa Daban daban na Duniya.

ya jaddada Bukatar Dake akwai ga gwamnti da sauran masu ruwa dantsaki su Saka hannun jrinsu a bangaren wasanni don tallafawa matasan Yan Wasa wadanda suke fatan Zama manyan yan Wasa a rayuwarsu ta kwallo.

Da yake tsokaci amadadin tawagar Arewa maso yamma, Sakataren kungiyar YSFON a jihar Kebbi Kuma na shirye shirye a shiyyar Arewa Maso yamma Har Ila yau Mai baiwa Gwamnan jihar Kebbi shawara Akan wasanni, Alhaji Babangida Sarki Wanda ya bayyana Farin cikinsa bisa kokarin yan Wasan su Duk kuwa Da rashin nasara Da sukayi a wasan karshe ya bukaci Yan Wasan Da su Yi hakuri Domin kuwa a kwallan kafa dole ne Kaci watarana a cika.

Abdulgaffar Wanda yayi jawabi a madadin Sakataren kungiyar YSFON a kaduna Abdulrazak Usman ya ce an zabi wasu Yan Wasa a lokacin wannnan gasa Kuma zasu  jihar Kaduna zuwa Kebbi Domin halartr Wani wasan Mai muhinmanci Inda wasu Turawa Ke dako Domin su zabi hazikan Yan Wasa zuwa nahiyar Turai.

Yayin Da a wasan niman Na uku tawagar Arewa ta tsakiyar ce ta lashe Bayan doke tawagar kudu maso kudu a bugun Daga kai Sai Mai tsaran raga yayin Da Kuma kudu maso kudu ta kammala a matsayi ta hudu.

Dan wasan gaba na tawagar Arewa maso yamma Wanda ya fito Daga jihar Kebbi Hayatu Mula shine ya lshe kyautar Wanda yafi zura kwallo a raga Da guda takwas yayin Da Adamu Ibrahim na tawagar Arewa maso gabas ne ya Zama mai tsaran raga mafi kokari Sai Kumar Bashir Muhammad yafi Kowa taka Leda.


Usman Ibrahim....



Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma