Karamar Hukumar Chikun ta tallafawa Matasa Sama da 200 da Naira Miliyan 6

 



25th July, 2024

Daga Usman Ibrahim.


Shugaban Karamar Hukumar Chikun Mr Salasi Nuhu Musa ya dauki Nauyin Matasa maza da mata sama da Dari biyu da aka koya musu Sana'oi daban daban.

A wata Sanarwa da mai Taimaka masa akan yada Labaran a kafafen zamani, Jim Gami Makama ya fitar, Mr Salasi ya Musu Alkawarin Naira Miliyan Shida ga matasa 200 da aka yaye Domin su fara sana'oin su da shi.

Ma'aikatar Kwadago da Samar da ayyukanyi ta Kasa ce ta koyawa matasan Sana'oi a Cibiyar koyon sana'oi dake nan Kaduna.

Kawo yanzu a kashin Farko ta nauki Nauyin matasa 50 sai kashi na Biyu matasa 110 a kashi na uku an horas da matasa 200 sai kashi na hudu aka horas da Matasa 200.

Yanzu haka Shugaban Karamar Hukumar Chikun Injiniya Salasi Nuhu Musa ya dauki nauyin koyawa  Matasa 560 sana'oi kenan run bayan Hawansa Shugabancin karamar hukumar.

labaran YCMC MEDIA









Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma