Golden Boys kawo ta Lashe Seyi Tinubu Kawo December Cup 2024 bayan Doke Tornadoes
13 Janairu, 2025
Daga Usman Ibrahim Mahuta
Kungiyar kwallon kafa ta Golden Boys Fc dake Kawo Kaduna ta lashe gasar cin kofin zaman lafiya wanda Seyi Tinubu ya dauki nauyi na Kawo December Cup bayan data doke Kawo Tornadoes da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaran raga a wasan karshen.
Golden Boys ce ta fara zura kwallo jim kadan da fara wasan amma kafin aje hutun rabin lokacin Abdulazeez Butu na Kawo Tornadoes mai maida wasan 1-1 a a Zangon farko na wasan bayan da suka samu finareti inda daga nan ne aka je bugun daga kai sai mai tsaran raga.
Yan wasan Tornadoes biyu sun barar da kwallo biyu wanda hakan ya baiwa Golden Boys lashe gasar.
Da yake jawabi a lokacin wasan, Babban mai baiwa shugaban kasa Tinubu shawara akan hulda da al’umma a yankin arewa maso gabas,, Abdulhameed Yahaya Abba ya yabawa Seyi Tinubu da kwamitin shirya gasar bisa kokarin su inda ya kara da cewa sannu a hankali gasar na dawo da martabar kwallon kafa a jihar kaduna.
Suma a jawabin su, shugaban karamar hukumar kaduna ta arewa, Muhammad Gambo Zion da shugaban kungiyar masu rusu ruwa da tsaki na APC, Abdulazeez Kaka dama daya daga cikin shugabannin gudanarwa na kwalejin ilimi ta tarayya dake Potiskum, Mr Nasiru Bala ja'oji sun bayyana gasar a matsayin Babban nasara ga ci gaban wasannin a cikin al’umma.
A jawabinshi na maraba, shugaban shirya gasar ga Seyi Tinubu, Musa Ibrahim ya godewa Mr. Seyi Tinubu da kungiyoyin da suka fafata gasar da daukacin yan kallo da suka bada lokacin su tun daga farkon gasar har karshe wajen ganin an kammala lafiya.
Baya ga lashe kyautar naira dubu 250,000 zakarun gasar Golden Boys ta samu gudunmuwar kudi naira Miliyan biyar daga Mr Nasiru Bala ja'oji da kuma sauran wadanda suka bada nasu gudunmuwar irin su, SSA Abdulhameed Yahaya Abba da Jarumar Matan Kasar Hausa Hajiya, Umma Isah Galadima da dai sauran su.
Sauran manyan baki da suka halarci wasan karshen sun hada da, mai girma Hakimin kawo Alhaji Jibril Muhammad Magaji, da Aliyu Abdulrahman Haruna Chakis da dan majalisar tarayya mai wakiltar kaduna ta kudu, Alhaji Hussaini Kero da tsohon dan wasan Super eagles, Garba Lawal da dai sauran wadanda aka gayyata.
Idan dai za a iya tunawa an fara gasar ne tun a watan Nuwanban 2024 kuma kungiyoyin kwallon kafa 32 suka fafata wanda Mr. Seyi Tinubu ya dauki nauyi.

Comments
Post a Comment