Hon. Nasiru Ja’oji ya baiwa Golden Boys kawo Miliyan 5 bayan lashe gasar Seyi Tinubu kawo December Cup na 2024.


 

13 Janairu, 2025

Daga Usman Ibrahim Mahuta 

A wani kokari na tallafawa bangaren wasanni a yankunan karkara, daya daga cikin shugabannin gudanarwa na kwalejin ilimi ta tarayya dake Potiskum a jihar Yobe, Mr Nasiru Bala ja'oji ya bada gudunmuwar kudi har naira miliyan biyar ga kungiyar kwallon kafa ta Golden Boys Fc dake Kawo a jihar kaduna.

Mr Nasiru Ja’oji ya bada wannan gudunmuwa ne a lokacin da yake jawabi wajen wasan karshe na gasar December cup na kawo na 2024 wanda Seyi Tinubu ya dauki nauyi.

Ya bayyana cewa gasar ya samar da dama ga yan wasan domin bayyana irin baiwar da ubangiji ya musu a bangaren wasan kwallon kafa yana mai cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a shirye take wajen tallafawa matasa a wannan bangare na wasanni.

Bala Ja’oji ya kuma jinjinawa shugaban shirya gasar na Seyi Tinubu wato Musa Ibrahim bisa kokarin sa na hada kan al’ummar jihar kaduna inda ya bayyana shi a matsayin Babban nasara ga jama’a.

Da yake jawabi akan irin tallafin da Seyi Tinubu ke baiwa matasa, Ja’oji ya bayyana yakinin cewa ganin irin wannan karamcin da Seyi Tinubu zai matukar taimakwa matasa idan aka fadadashi zuwa wasu yankunan kasarnan.

Ya kuma yi kira ga yan Najeriya su ci gaba da marawa Gwamnatin dake ci yanzu baya don ci gaban tattalin arzikin kasarnan baki daya.


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

Brazil ta Doke Najeriya da ci 1-0