Wakilin Sarkin Zuru ya Bukaci Samar da Cibiyoyin koyon Sana'oi



 Daga Usman Ibrahim Mahuta 

3 ga Watan Fabarerun 2025.

An bukaci a samar da Karin Cibiyoyin koyon Sana'oi a Cikin Al'umma.

Mai Girma wakilin Sarkin Zuru na Jihar Kaduna, Engineer Zubairu Kabir Danjuma ya bukaci Shugabannin da Sauran Masu Hannu da shuni su samar da Cibiyoyin koyon Sana'oi ga Matasa domin rage yawan zaman kashe Wando  Cikin Al'umma.

Engineer Zubairu Kabir Danjuma ya bukaci hakan ne a lokacin da yake jawabi Wajen yaye dalibai Hudu da Suka Kammala koyon Aikin Dinki a garin Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna Wanda kungiyar Teloli na Mahuta ta shirya .

Mai Girma wakilin Sarkin Zuru, ya bayyana Cewa matukar aka samar da Wuraren koyon Sana'oi zai taimaka ba kadanba domin kuwa Mata da Matasa zasu Samu aikinyi.

Engineer Zubairu Kabir ya kuma shawarci Matasa da su kaucewa jiran Aikin Gwamnati a maimakon haka su Rungumi Sana'oin hannu domin shine kadai Hanya mafita Wanda zai su rike kansu.

Ya Kuma jinjinawa kungiyar Teloli na Mahuta karkashin shugabancin Malam Kabir Muhammad bisa Kokarin da sukeyi wajen koyawa Yara Sana'oi inda a cewarsa Allah ne kawai zai biyasu.

Da yake Jan hankalin daliban da aka yaye, Wakilin Sarkin Zuru Engineer Zubairu Kabir Danjuma ya kalubalancesu dasu ji Tsoron Allah a Cikin ayyukansu su kuma Rika Cika Alkawari idan aka basu Aiki.

A karshe Mai Girma wakilin Sarkin Zuru na Jihar Kaduna Engineer Zubairu Kabir Danjuma yayi Alkawarin Tallafawa yaran da aka yaye domin Suma su Dogara da kansu.




Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

Brazil ta Doke Najeriya da ci 1-0