Allah ya yiwa Sheik Shehu Usman Rigi-Rigi rasuwa
2 ga Janairu, 2026
Labari daga Abubakar Dan Yaro
Innalillahi wainnailaihirrajiun:
Allah ya yiwa Fitacccen Malamin Addinin Musulunci nan a Jihar Kaduna, Sheik Shehu Usman Idriss wanda aka fi Sani da Regi-regi na Manzon Allah.
Kafin rasuwarsa Malamin ya shahara Wajen sanya mabiyansa da Sauran Al'ummar Musulmai nishadi Saboda salon wa'azinsa.
Shiek Shehu Usman ya rasu ya bar Matansa 4 da yara 37 da jikoki da dama
Za'a gudanar da Jana'izarsa da Karfe 4:30pm na yammacin yau idan Allah ya kaimu a Gidansa dake Kusfa Zaria.
Da Fatan Allah ya gafarta Masa da Rahama Amin.

Comments
Post a Comment