Dan wasan Najeriya Gabriel Orok ya sanya hannu a kungiyar Al Swehli ta Kasar Libya daga Emyimba FC.
Gabriel
Orok ya sanya hannu a kungiyar Al Swehli ta Kasar Libya daga Emyimba FC.
2
ga Janairu, 2026
Daga
Usman Ibrahim.
Dan
wasan gefe na Najeriya Gabriel Orok
ya kammala komawarsa dindindin zuwa ƙungiyar Al Swehli ta ƙasar Libya.
Gabriel
ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku
da ƙungiyar ta Arewacin Afirka.
Tsohon
ɗan wasan Enyimba FC ya kammala sauya shekan ne bayan ya yi nasarar gwajin
lafiya tare da cimma matsaya kan sharuɗɗan kwantaragin da kulob ɗin.
Al
Swehli ta riga ta gabatar da Orok a hukumance, tana mai tabbatar da isowarsa
gabanin kakar wasa mai zuwa.
Sauyin
da Orok ya yi alama ce ta buɗe sabon babi a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa,
kasancewar wannan ne karon farko da zai taka leda a Arewacin Afirka.
Ana
sa ran ƙwarewarsa ta gudu, kai hari kai tsaye da iya kutsa kai za su ƙara wa sabuwar
kungiyarsa Al Swehli ƙarfi a ɓangaren gefe wajen rika kai kora.
Zaku
Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka.
Facebook
YCMC News
You
Tube YCMC News
Tit
Tok YCMC News

Comments
Post a Comment