MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma

 




1 Janairun, 2026

Daga Usman Ibrahim Mahuta 

A daidai lokacin da ake tunkarar babban taron Jam'iyyar APC na Kasa, Matasa daga Shiyyar Arewa maso Yamma na ci gaba da bayyana ra'ayin su na tsayawa takara a matakai daban daban.

Na kwana kwanannan shine, Muhammad Abubakar Mal-moh Wanda ya bayyana aniyarsa na tsayawa takaran Shugaban Matasa na Jam'iyyar APC a Shiyyar Arewa maso Yamma.

Taron ya gudana ne Jihar Kaduna inda magoya bayan Muhammad Abubakar Mal-Moh suka  taru domin shaida ayyana kudirinsa na tsayawa takarar Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, gabanin babban taron kasa na jam’iyyar da ke tafe.

Da yake bayyana kudirinsa, Muhammad Abubakar Mal-Moh ya ce shawarar da ya yanke ta biyo bayan tuntuba mai zurfi da ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a matakin jiha da na kasa, musamman matasa.

Ya bayyana cewa Shirin MAL-MOH an kirkire shi ne domin tallafawa kokarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani wajen karfafa gwiwa da bunkasa rayuwar matasa, tare da karfafa ci gaban jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma.

Da take jawabi a wajen taron, Babbar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna kan Harkokin Dalibai, Hajiya Amina Sani Bello, ta bayyana kudirin a matsayin wanda ya dace ya kuma zo akan lokaci, tana mai cewa tarihin ayyukan Muhammad Abubakar Mal-Moh a jam’iyyar ya nuna cewa mutum ne nagari kuma abin dogaro da zai iya jagoranci.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana kwarin gwiwa kan salon jagorancinsa, suna masu cewa zai iya wakiltar muradun matasa yadda ya kamata tare da bayar da gudummawa mai ma’ana wajen bunkasa jam’iyyar.

Bayan kammala ayyana kudirin, Hajiya Amina Sani Bello ta mika tutar jam’iyyar APC ga dan takarar, alamar goyon bayan Gwamnan Jihar Kaduna.


Usman Ibrahim Mahuta 

Zaku iya bibiyarmu a shafukanmu kamar haka.

Facebook YCMC NEWS 

You tube YCMC NEWS 

Tik Tok YCMC NEWS 


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.