Rundunar sojin Najeriya ta kashe mataimakin shugaban Boko Haram a Jihar Borno
Rundunar soji ta kashe mataimakin shugaban Boko Haram
2 ga Janairu, 2026
Daga Usman Ibrahim
Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe wani babban jagoran
Boko Haram, wanda aka bayyana shi a matsayin mataimaki na biyu tare da wasu
mayaka goma a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
An
bada rahoton cewa an kashe ‘yan ta’addan ne a yankin Komala da ke Ƙaramar
Hukumar Konduga yayin wani samame da rundunar ta kai da daddare.
A
cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar,
Laftanar Kanal Sanni
Uba ya fitar, ta ce an kuma kwato makamai da dama daga hannun yan ta’addan.
Ya
ce lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan da sojoji suka hallaka fitaccen kwamandan
Boko Haram da ISWAP, Julaibib a yankin Gujba na Timbuktu Triangle.
Ya
ƙara da cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar da harsasai da kekuna da
kayayyakin abinci da kuma magunguna masu yawan gaske.
Zaku
Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka.
Facebook
YCMC News
You
Tube YCMC News
Tit
Tok YCMC News

Comments
Post a Comment