Gasar YSFON firimiya Kaduna Mako Na 4


Za a ci gaba Da gasar YSFON premiya Lig Na Kaduna Da wasannin mako Na hudu 4.

A juma'arnan kungiyar kwallon kafa ta Junior Kaduna United zata fafata Da New City football Club a filin wasa Na SMC Da karfe 4pm ita kuwa Katabu United zata Karbi bakuncin Soccer Stars a filin wasa Na Nagarta Dake Maraban Jos Da karfe 4pm Sai  Bakura United itama zata kece Raini Da  Fancy Stars a filin minista Da karfe 4pm Na yamma.

Yayin Da a ranar Asabar, Young Barcelona zata Karbi bakuncin DAFA a filin wasa na Kargi Da karfe 4pm Na yamma Sai Nanasco f c ta Rigasa zata Kara Da Kwaru United a filin wasa Na NIPOST kurmin mashi Da karfe 4pm Na yamma.

Sai wasannin ranar Lahadi, FC Hearts zata buga Da Rigachikun Football Academy a filin yankin ruwa wato Water Tank , Rigasa Da karfe 4pm ita kuwa Danmani United zata fafata Da Soccer Campus a filin NIPOST Da karfe 4pm Na yamma Sai a karshe Alausa Babes Da fafata wasa Da Arewa Youth a filin wasa na Maimuna Gwarzofootball Suma Da karfe 4 Na yammaci.

A Wani labarin Kuma, hukumar ta YSFON tana cika shekaru 58 Da Kaduna kawo yanzu.

Anan Muna Taya daukacin masu fafata wannan gasa.


Usman Ibrahim............

Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.

Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.