Henry ya bukaci Messi ya Koma Barcelona


 

Tsohon Dan wasan Arsenal, Barcelona Da Faransa Thierry Henry ya Na bukatar Lionel Messi ya Koma tsohuwar kungiyar sa ta Barcelona ya Kuma ajiye tamola a filin wasa Na Nou Camp.

wannan Na zuwa ne Bayan Da Magoya bayan PSG suka yiwa Messi ihu a makon Daya gabata Wanda Hakan Bai yiwa Henry Dadi ba.

Thierry Henry yace ya zaku yaga  Lionel Messi ya kammala buga Wasa a Barcelona saboda Hakan ya kamata.

kwamtiragin Messi a PSG Zai Kare ne a karshen Watan yunin wannan shekarar.

Henry yace ihun Da Magoya bayan PSG sukayiwa Messi a wasan da kungiyar ta Yi rashin nasara Akan Lyon Bai dace ba.

Thierry Henry  ya bayyana bacin ransa Akan matakin Da suka dauka.

Rahotanni Sun bayyana cewa magoya bayan PSG Suna fushi ne Na rashin samun nasara Akan Bayern Munich a gasar Zakarun Nahiyar Turai adon haka Suna ganin Kawai sun gaji DA Messi ya bar kungiyar.

Henry, Wanda ya taba taka Leda Da Messi a  Barcelona,  ya ce komawar Shi Barcelona ne Kawai mafita.


 Usman Ibrahim.......


Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma