Albash FC ta Doke Zaragoza F c a Gasar Ex ministers December Cup
Gasar Ex minister December Cup Kaduna.
Daga Usman Ibrahim Mahuta.
kungiyar kwallon kafa ta Albash Football Academy ta Samu Nasarar zuwa wasan karshe na Gasar Ex ministers December Cup sau biyu a jere bayan data doke Zaragoza F c da ci 1-0 a wasan semi final.
Wasan Daya Gudana a Talatarnan ya Samu Halartar Dandazon Yan Kallo inda Suka nishadantu da Wasannin.
Bisa Wannan Nasara ne, Kungiyar kwallon kafa ta Albash Academy zata kara da Sharp shooters F c a wasan karshe domin lashe Gasar.
A cewar Shugaban kwamitin Shirya Gasar, Coach Bakura Muhammad an tsara fafata wasan karshen ne idan Allah ya kaimu ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025 da yammaci a Filin wasa na Minister Unguwar Sarki Kaduna
Coach Bakura ya kuma yabawa Kungiyoyi 16 da Suka fafata Gasar bisa Gudunmuwa da Hadin kai da Suka Bada Wajen Samun Nasarar zuwa wasan karshe Lafiya inda kuma ya bukaci su dore a hakan don ci gaban Wasannin a Jihar Kaduna.

Comments
Post a Comment