Northwell Academy ta Lashe Gasar W/ Sarkin Zuru December Cup U14 Mahuta sau biyu a Jere


 25 ga Watan Janairun 2025

Daga Usman Ibrahim Mahuta.


Kungiyar kwallon kafa ta Northwell Football Academy Makera dake Karamar hukumar Kaduna ta Kudu ta lashe Gasar December Cup Wanda Wakilin Sarkin Zuru na Jihar Kaduna Injiniya Zubairu Kabir Danjuma ya Shiryawa Matasa Yan Kasa da shekaru 14 a Mahuta.

Northwell ta doke kungiyar kwallon kafa ta Lion Stars Football Club ne. da ci 3-2 a wasan karshe da Suka Buga a Asabar Dinnan kuma ya lashe Gasar sau biyu a jere kenan.

Idan za a iya tunawa, a shekarar 2024 Northwell ce ta Doke Kungiyar kwallon kafa ta Athletic Academy a wasan karshe kuma ta Lashe Gasar.

Dan wasan tsakiya Abdullatif Tajudeen shine ya lashe kyautar mafi kwazo a Kananan Yara sai Simon Friday ya lashe kyautar Wanda ya fi kowa Zura kwallo da guda hudu yayin da aka baiwa Daukacin kungiyoyin da Suka fafata a Gasar takardar Shaidar fafatawa a Gasar.

Mai Girma wakilin Sarkin Zuru ya nuna Farin Cikin sa bisa irin Yan wasan Daya ganewa idanunsa Yana Mai jaddada muhinmancin wasan kwallon kafa musanman yadda ta zama Hanyar Samun Kudi a yanzu.

Sauran Wadanda Suka halarci wasan karshen sun Hada da Mai Girma wakilin Mahuta Alhaji Yahuza Ibrahim da Shugaban Kungiyar DMF Football Academy Malam Dahiru Musa da sauran Manyan Baki da Suka fito daga sassa Daban daban na Jihar Kaduna.



Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

Brazil ta Doke Najeriya da ci 1-0