TA TABBATA: Hukumar La Liga ta yiwa Dani Olmo da Pau Victor Rijista.
9 ga Watan Janairun 2025
Daga Usman Ibrahim Mahuta.
TA TABBATA: Hukumar La Liga ta tabbatar da yiwa Yan wasan Barcelona Dani Olmo da Pau Victor Rijista.
A ranar Laraba ne aka amincewa Barcelona ta yiwa Dani Olmo da Pau Victor Rijista kuma Sa'oi kadan hukumar La Liga ta tabbatar da Rijistan
Idan Za a iya tunawa, Hukumonin La Liga da na kwallon kafa ta kasar Spaniya sukaita yin watsi tare da kin amincewa da yiwa Olmo da Victor rijista.
Wannan Labari Mai Dadi ne ga yan Barcelona kuma a yanzu Yan wasan biyu, Olmo da Victor za su iya fafata wasan karshe na Spanish Super Cup tsakaninsu da Real Madrid a ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025.
Yan wasan biyu za su ci gaba da Buga Wasa har na tsawon Watanni uku Koda yake za a kara tsawaita lokacin bugawarsu har zuwa Karshen Wannan kakar Wasa idan Suka ci ga ba da yin Nasara a karar da Suka shigar.

Comments
Post a Comment