An bukaci Teloli su Rika Cika Alkawari gabanin Azumin Watan Ramadan.
Daga Usman Ibrahim Mahuta
5 ga Watan Fabarerun 2025
An bukaci Teloli su Rika Cika Alkawari gabanin Azumin Watan Ramadan.
A dai dai lokacin da Watan Azumin Ramadan ke kara kawo jiki, an Bukaci Teloli da su Rika Cika Alkawari idan an basu Dinki don biyan bukatun Al'umma.
Mai Girma wakilin Mahuta Alhaji Yahuza Ibrahim ne yayi Kiran a lokacin da yake jawabi Wajen yaye dalibai Hudu da Suka Kammala koyon Aikin Dinki a garin Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Alhaji Yahuza Ibrahim ya ce ta Hanyar Cika Alkawari ne Sana'arsu dama kimarsu da jarajarsu zai daukaka a idan duniya yayin kuma ya ja hankalin Masu Bada Dinki su Rika biyan Telolin Hakkokinsu.
A nashi jawabin, Mai Girma Sarkin Yakin Mahuta Dr Jafaru Bello Dambazau Wanda ya Samu wakilcin Malam Hussaini Mustapha ya nuna farin Cikin sa bisa Wannan Nasara da aka Samu Yana Mai Shan Alwashin bata tasa Gudunmuwar Wajen Bunkasa Sana'oi.
Da yake jawabi akan Muhinmancin Sana'oi a tsakanin Matasa, Daya daga Cikin Shugabannin Matasa na Mahuta, Malam Salis Musa ya kalubalanci Iyayen Yara da su Rika sanya yaransu a Sana'oin hannu don su Samu abin dogaro da kai.
Su kuwa tsaffin Teloli na Mahuta, Malam Dahiru Musa da Malam Abubakar wanda aka fi sani da Baba Titi sun yi kirane ga Telolin yanzu su Dauki Sana'ar da Muhinmanci Saboda tana da Tarihi sosai ko a Musulunce.
Daya daga Cikin Iyayen Yaran da aka yaye, Malam Muhammad ya yabawa Shugabannin yaran bisa hakurin da sukayi har aka cimma wannan Nasara inda Suka yi Addu'ar Allah ya Saka Musu da mafi Alkhairi.
Sauran Wadanda Suka halarci taron, sun Hada da Mataimakin Shugaban Kungiyar Teloli na Mando B .....da Sakataren kungiyar......da Tsohon Ma'ajin kungiyar dama Daya daga Cikin Shugabannin Matasa na Mahuta Auwal S Munkaila wato TM wanda ya Samu Wakilcin Muhammad Aliyu Abidoka da dai sauran Yan uwa da abokanan Arziki.
A Karshen taron Bikin an gabatar da shahada ga Dalibai Hudu da Suka Kammala koyon Aikin Dinki Wanda ke nuna Fara Cin gashin kansu.





Comments
Post a Comment