NPFL Mako na 24, Rangers ta doke Kano Pillars, Katsina United ta doke Abia Warriors

 




Sakamakon wasannin gasar Kwararru ta kasa bayan kammala wasannin mako na 24.

2 ga Janairun, 2026

Daga Usman Ibrahim.

Sakamakon wasannin da aka buga mako na 24 na gasar kwararru ta kasa wato (NPFL) a ranar Lahadi a filaye daban-daban.

Rangers International ta doke Kano Pillars da ci 2–0 sai Katsina United ma ta samu nasara akan Abia Warriors da ci 2–0 yayin da
Bayelsa United ta sha kashi da ci 1–0 a hannun Enyimba.

Sauran sakamakon wasannin sun nuna cewa Wikki Tourists da Nasarawa United sun tashi canjaras wato 1–1 sai kuma Niger Tornadoes ta yi canjaras 2–2 da Bendel Insurance.

Haka kuma a Litinin dinnan za’a fafata sauran wasannin mako na 24 inda El-Kanemi Warriors za ta karɓi baƙuncin Kun Khalifat sai Barau FC Kano za ta fafata da Ikorodu City a Filin Wasa na tunawa da Marigayi Sani Abacha sai Kwara United za ta kara da Warri Wolves yayin da Remo Stars za ta gwabza da Plateau United.

Idan muka duba teburin gasarkuwa, a  halin yanzu Rivers United c eke ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 41 sai
Nasarawa United ta biyu da maki 40 yayin da Rangers International ke matsayi na uku da maki 39 sai Ikorodu City da Abia Warriors da ke matsayi na huɗu da na biyar da maki 38 kowannensu.

Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka.

Facebook YCMC News

You Tube YCMC News

Tit Tok YCMC News




Comments

Popular posts from this blog

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.

Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.