Hon. Dauda Madaki ya Jaddada Aniyar Gwamnatin sa wajen Inganta tsarin Shugabanci ta hanyar anfani da Sahihan Bayanai.

 


HON. DAUDA MADAKI YA JADDADA ANIYAR GWAMNATINSA NA INGANTA TSARIN SHUGABANCI TA HANYAR AMFANI DA SAHIHAN BAYANAI.

Daga, Usman Ibrahim Mahuta.

5 ga watan Ogustan, 2026.

Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Kajuru, Honorable Dauda Madaki ya bayyana cewa gwamnatin sa zata ci gaba da barin kofarta a bude wajen gudanar da harkokin Shugabanci ga Al'umma don ci gaba.

Dauda Madaki ya bayyana haka ne a cikin wata Sanarwa data samu Sanya hannun Sakataren yada labaran sa, Mr. John Ezra Sojah.

Hukumar kula da kasafi da tsare-tsare ta Jihar kaduna tare da hadin gwiwar Hukumar UNICEF Ofishin kaduna ne suka shirya taron karawar Juna sanin na kwanaki Uku ga Shugabannin kananan Hukumomin Jihar kaduna a taron daya gudana a Jihar Kano.

A cewar Sanarwar, Dauda Madaki ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin sa na ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Kaduna da UNICEF da sauran abokan hulɗar domin ƙarfafa ƙwarewar hukumomi, bunƙasa shugabanci mai haɗa kowa da kowa, da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwa da walwalar al'umma.

Har ila yau, a lokacin taron shugabannin ƙananan hukumomin sun gabatar da alkawuran aikace-aikace da nufin ƙarfafa tsarin shugabanci da inganta samar da muhimman ayyukan jin daɗin al'umma a matakin karkara.

Sun kuma bayyana dabarun tabbatar da amfani da sahihan bayanai wajen tsara manufofi, inganta hanyoyin sauraron ra'ayoyin jama'a, da ƙara bayyana gaskiya a harkokin gudanar da mulki.

Taron har ila yau, ya jaddada muhimmancin gudanar da nazarin ayyuka akai-akai a fannoni kamar kula da Lafiya da Gina Jiki da Ilimi da Kariya ta Zamantakewa da da Ruwa da tsafta da Muhalli a matsayin ginshiƙan cimma ci gaba mai ɗorewa a matakin ƙananan hukumomi.

Usman Ibrahim 

YCMC News.


Comments

Popular posts from this blog

Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.

Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.