Young Spiders ta lashe Gasar cin kofin Zaman Lafiya na Gwamna Uba Sani
Daga Usman Ibrahim
9 ga watan Ogustan, 2026.
An gudanar da wasan ƙarshen ne a filin wasa na Kajuru Township Stadium, inda dimbin masoya ƙwallon ƙafa, shugabannin al'umma, jami'an gwamnati da sauran manyan baƙi daga ciki da wajen ƙaramar hukumar suka halarta.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Muhammad Shuaibu, ne ya shirya gasar da nufin inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummomi daban-daban na yankin, tare da nuna goyon baya ga gwamnatin Gwamna Uba Sani.
Young Spiders ce ta fara samun damar cin ƙwallo, inda Sagiru Gambo ya buɗe ƙwallon a minti na 12, bayan da ya samu damar zura ƙwallon a raga.
Ana tsaka da wasa ne Alkalin wasa ya ba Kufana United bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da Dan wasan bayan Young Spiders ya yi keta amma Alex Charles ya kasa zura kwallan a raga.
Young Spiders ta ci gaba da matsa lamba, inda a mintuna kadan kafin a tafi hutun rabin lokaci ne, Izziden Adamu ya maida wasan 2 da nima Wanda yasa Young Spiders ta ci gaba da Jan ragamar wasan.
Duk da cewa an baiwa Dan wasan Young Spiders jan kati bayan samun katin gargadi na biyu wanda ya kai ga korarsa daga fili, ƙungiyar ta iya riƙe ragamar wasan har zuwa ƙarshen mintuna 90, inda ta samu nasarar doke Kufana United da ci 2–0 tare da ɗaga kofin gasar.
Da yake Jawabi lokacin wasan, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Dr. Dauda Madaki, ya yabawa waɗanda suka shirya gasar bisa ƙoƙarinsu na inganta zaman lafiya da kuma tallafa wa matasa ta hanyar wasanni.
A nasa jawabin, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Mazabar Kajuru, Danlami Stingo, ya bayyana gasar a matsayin abin da zai taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al'ummomin Kajuru.
Shi ma Wanda ya shirya gasar kuma Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Muhammad Shuaibu, ya ce an shirya gasar ne domin ƙarfafa zaman lafiya tsakanin al'ummomi, tare da nuna godiya da kuma goyon baya ga ƙoƙarin Gwamna Uba Sani na kawo ci gaba ga Matasa.
Young Spiders Kasuwan Magani, wadda ta zama zakara da Kufana United wadda ta zo ta biyu, da Mountain Strikers ta Kajuru wadda ta zo ta uku, duk karbi kofuna da kuma kyaututtukan kuɗi da Wanda Dan Majalisar Tarayya, Fedelix Bagudu da Dr. Dauda Madaki da Danlami Stingo da dukkan Kansiloli goma na Kajuru suka bayar.
An kuma bayar da kyaututtukan gwarzon ɗan wasa, inda Ahmad Abdullahi ya lashe kyautar Mafi Kyawun Mai Tsaron raga, yayin da Mubarak Isma'il ya zama wanda ya fi kowa yawan cin ƙwallaye.
Haka kuma, Izziden Adamu ya lashe kyautar Gwarzon Ɗan Wasan Gasar.
An kuma bai wa wasu manyan baki da suka halarci taron lambobin yabo, domin girmama irin gudunmawarsu da goyon bayan da suke bai wa ci gaban karamar Hukumar Kajuru.
Wasan ƙarshen ya samu halartar dimbin jama'a, inda aka gudanar da shi cikin yanayi na farin ciki da annashuwa, tare da haɗa al'ummomi daban-daban na Kajuru ta hanyar ƙwallon ƙafa, cikin kyakkyawar yanayina zaman lafiya, haɗin kai da kyakkyawar mu'amala ta wasanni dama gudunmuwar Jami'an tsaro.




Comments
Post a Comment