Tawagar Arewa maso gabas ta lashe gasar YSFON Na kasa Bayan doke Arewa maso yamma a wasan karshe
Tawagar kwallon kafa ta YSFON Na shiyyar Arewa Maso gabas ta lashe gasar YSFON U-16 na kasa Da aka kammala a jihar Kaduna Bayan doke shiyyar Arewa Maso yamma daci Daya mai ban haushi a wasan karshe. Wasan karshen Wanda ya gudana a filin wasa Na Ahmadu Bello Dake nan Kaduna ya Samu halartar manyan baki Da suka fito Daga bangarori daban daban Da sauran yan kallo Da suka fito Domin Shaida gasar na kasa. Dan wasan Arewa maso gabas Abdulrahman Ali shine ya zura kwallo guda data makale tun kafin aje Hutun Rabin lokaci Na wasan a gaban Yan kallo musanman magoya bayan shiyyar Arewa Maso yamma. Tawagar Arewa Maso yamma ta rinka matsa lamba wa tawagar Arewa maso gabas Dan ganin ta Rama kwallon Amma kokari Da jajurewa Na mai tsaran raga Na tawagar Arewa maso gabas Adamu Ibrahim yasa an gaza Rama kwallon Kuma tawagar Arewa maso gabas ce ta lashe gasar. Da yake jawabi Bayan Mika kofin GA Wanda suka lashe, Kwantrola na hukumar shige Da fice ta kasa reshen jihar Kaduna,Bashir Muhammad Lawal ya ...