Posts

Ministry of Labour and Employment trains over 200 youths on Vocational Skills

Image
  25th July, 2024 Chikun Local Government empowers over 200 youths on Vocational Skills. In its continuous effort to provide Job opportunities among youth across the Country, the federal Government has trained over two hundred youth on various skills in kaduna state. The training which is under the National Vocational Skills training and empowerment program was organised by the federal Ministry of Labour and Employment kaduna state office. The National Vocational Skills training and empowerment program was introduced by the Federal Government with the aim of reducing the rate of unemployment among youth across the Country. Speaking during the Graduation, the deputy director, Training Development who represented the Minister of state for Labour and Employment, Nkiruka Onyejeoka, Engineer Ojo Sunday, described the training as a huge success to the nation that will address youth restivenes. Emphasizing on the important of training the youth, the Controller, federal Ministry of Labour ...

Brazil ta Doke Najeriya da ci 1-0

Image
 25th July, 2024 Daga Usman Ibrahim Tawagar Super Falcons ta kasa ta yii Rashin nasara a wasanta na Farko a gasar Olympic a hannun kasar Brazil da ci 1-0 shekaru 16  rabonta da fafatawa a gasar. Wasan da aka buga a Alhamis Dinnan a Birnin Bordeaux dai ya tattara yan kallo kuma Najeriya tayi Rashin Nasara a wasan na rukuni na uku.    LABARAN YCMC

Karamar Hukumar Chikun ta tallafawa Matasa Sama da 200 da Naira Miliyan 6

Image
  25th July, 2024 Daga Usman Ibrahim. Shugaban Karamar Hukumar Chikun Mr Salasi Nuhu Musa ya dauki Nauyin Matasa maza da mata sama da Dari biyu da aka koya musu Sana'oi daban daban. A wata Sanarwa da mai Taimaka masa akan yada Labaran a kafafen zamani, Jim Gami Makama ya fitar, Mr Salasi ya Musu Alkawarin Naira Miliyan Shida ga matasa 200 da aka yaye Domin su fara sana'oin su da shi. Ma'aikatar Kwadago da Samar da ayyukanyi ta Kasa ce ta koyawa matasan Sana'oi a Cibiyar koyon sana'oi dake nan Kaduna. Kawo yanzu a kashin Farko ta nauki Nauyin matasa 50 sai kashi na Biyu matasa 110 a kashi na uku an horas da matasa 200 sai kashi na hudu aka horas da Matasa 200. Yanzu haka Shugaban Karamar Hukumar Chikun Injiniya Salasi Nuhu Musa ya dauki nauyin koyawa  Matasa 560 sana'oi kenan run bayan Hawansa Shugabancin karamar hukumar. labaran YCMC MEDIA

Shugaban NFF ya Bukaci a Daina Cunkusa Kalandar wasannin Premier ta Najeriya

Image
 Daga Usman Ibrahim... Gabanin Gasar kwararru ta kasa wato Nigeria premier league na kamar wasa ta 2024/2025, shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kasa, Alhaji Ibrahim Musa Gusau, ya bukaci Kwamitin shirya gasar daya daina Sanya wasannin da zasu Cunkushe wanda zai ci karo ko haifar da tarharo a lokacin gasar. Gusau ya bayyana hake ne yayin da Yake Jawabi a lokacin Babban Taron hukumar daya gudana a Abuja inda ya jaddada cewa a shirye suke wajen ganin gasar ya samu Gagarumin ci gaba . Ana saran Fara gasar Nigeria premier league ne a ranar Asabar 31 ga watan Ogustan 2024, inda masu Rike da Kambun gasar Rangers International zata kara da El-Kanemi Warriors a wasan Farko na Gasar. YCMC MEDIA.

Mr Olarewaju Lanre Ekundina Condoles with Families and Kajuru Emirate Council over the Death of District head Of Kajuru Alhaji Surajo Haruna.

Image
  By Usman Ibrahim........ 15th July, 2024. The Madubin Kajuru of Kajuru Emirate Council of kaduna State, Mr Olarewaju Lanre Ekundina has condoled with the Emir of Kajuru Alhaji Alhassan Adamu and the entire people of the Emirate over the Death of District Head of Kajuru Alhaji Surajo Haruna. Mr Olarewaju Lanre in his Condolence message to the Emirate Council, Described Late Alhaji Surajo Haruna as a Man of the people who has contributed Immensely to the Growth and development of Kajuru Emirate and the local Government as a whole. The Madubin Kajuru, Mr Olarewaju Lanre Ekundina who is also the Sadaukin Chikun and Danmajen Kufana prayed for the repose of the soul of the departed and comfort for all those who mourn this painful loss. The Madubin Kajuru Mr Olarewaju Lanre Ekundina also prayed to God to grant his soul eternal rest. Late Alhaji Surajo Haruna who passed away this Sunday evening has been the District Head of Kajuru since 2001 and later became the Ciroman Kajuru Emirate Co...

Gwamna Zulum ya baiwa Manoma Tallafi a Damasak.

Image
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar  Borno yayi alkawarin rage irin radadi na halin da alumma musanman manoma suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur a Damasak shalkwatar karamar hukumar Mobbar ta jihar domin bunkasa tsarin samar da wadataccen Abinci a jihar. Garin Damasak, daya ne daga cikin yankunan da jihar Borno ke alfahari dashi wajen samar da abinci, yankin sannu a hankali yana farfadowa bayan kwashe tsawon shekaru Suna cikin matsala sakamakon Rikicin kungiyar Boko Haram. Gwamnan na magana ne lokacin da yake ziyarar aiki na kwana biyu domin duba yadda ake raba kayan tallafi ga matan da suka rasa mazajen su da mata masu karamin karfi, ya kuma yi Alkawarin maida jihar Borno cikin jihohin da suka fita daga duk wata matsala ta karancin abinci a kasarnan. Ya kuma sha alwashin basu gudunmuwar Injin ban ruwa mai anfani da hasken Rana da iri na shuka da takin zamani a dai sauran kayayyakin aikin gona don ci gaban jihar. Daga Abubakar Abdullahi. Labaran YCMC media Kaduna.

Gamayyar kungiyoyin Arewa Sun koka akan tsadar kayan Masarufi

Image
  Talata 6-2-2024 7:00pm Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun bayyana damuwarsu akan yadda kayayyakin masarufi ke ci gaba da tashin gwauron zabi a fadin Kasarnan. Jaridar Daily Trust ta bada Rahoton cewa,  yan Najeriya daban daban suna ci gaba da nuna Damuwa da fargaba a sakamakon halin kunci da suke ciki sakamakon hauhawar farashin kayayyaki. Kamar su Shinkafa da Filawa da Siga da Siminti da dai sauransu kuma an danganta lamarin akan yadda farashin Naira ke ci gaba da faduwa a kasuwan cinikayyar kudi wanda hakan yasa alumma basa iya rayuwa cikin Natsuwa da wadata. A cikin wata Sanararwa da Shugaban Gamayyar kungiyar na kasa , Jamilu Aliyu Charanchi, ya fitar ya ce  lamarin ya kai yan Najeriya ga Bango matuka wanda ke bukatar a dauki kwararan matakai da suka da ce. Labaran YCMC media Kaduna.