Posts

Showing posts from January, 2025

Northwell Academy ta Lashe Gasar W/ Sarkin Zuru December Cup U14 Mahuta sau biyu a Jere

Image
 25 ga Watan Janairun 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta. Kungiyar kwallon kafa ta Northwell Football Academy Makera dake Karamar hukumar Kaduna ta Kudu ta lashe Gasar December Cup Wanda Wakilin Sarkin Zuru na Jihar Kaduna Injiniya Zubairu Kabir Danjuma ya Shiryawa Matasa Yan Kasa da shekaru 14 a Mahuta. Northwell ta doke kungiyar kwallon kafa ta Lion Stars Football Club ne. da ci 3-2 a wasan karshe da Suka Buga a Asabar Dinnan kuma ya lashe Gasar sau biyu a jere kenan. Idan za a iya tunawa, a shekarar 2024 Northwell ce ta Doke Kungiyar kwallon kafa ta Athletic Academy a wasan karshe kuma ta Lashe Gasar. Dan wasan tsakiya Abdullatif Tajudeen shine ya lashe kyautar mafi kwazo a Kananan Yara sai Simon Friday ya lashe kyautar Wanda ya fi kowa Zura kwallo da guda hudu yayin da aka baiwa Daukacin kungiyoyin da Suka fafata a Gasar takardar Shaidar fafatawa a Gasar. Mai Girma wakilin Sarkin Zuru ya nuna Farin Cikin sa bisa irin Yan wasan Daya ganewa idanunsa Yana Mai jaddada muhinmancin wasan...

Golden Boys kawo ta Lashe Seyi Tinubu Kawo December Cup 2024 bayan Doke Tornadoes

Image
 13 Janairu, 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta  Kungiyar kwallon kafa ta Golden Boys Fc dake Kawo Kaduna ta lashe gasar cin kofin zaman lafiya wanda Seyi Tinubu ya dauki nauyi na Kawo December Cup bayan data doke Kawo Tornadoes da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaran raga a wasan karshen. Golden Boys ce ta fara zura kwallo jim kadan da fara wasan amma kafin aje hutun rabin lokacin Abdulazeez Butu na Kawo Tornadoes mai maida wasan 1-1 a a Zangon farko na wasan bayan da suka samu finareti inda daga nan ne aka je bugun daga kai sai mai tsaran raga. Yan wasan Tornadoes biyu sun barar da kwallo biyu wanda hakan ya baiwa Golden Boys lashe gasar. Da yake jawabi a lokacin wasan, Babban mai baiwa shugaban kasa Tinubu shawara akan hulda da al’umma a yankin arewa maso gabas,, Abdulhameed Yahaya Abba ya yabawa Seyi Tinubu da kwamitin shirya gasar bisa kokarin su inda ya kara da cewa sannu a hankali gasar na dawo da martabar kwallon kafa a jihar kaduna. Suma a jawabin su, shugaban karamar h...

Hon. Nasiru Ja’oji ya baiwa Golden Boys kawo Miliyan 5 bayan lashe gasar Seyi Tinubu kawo December Cup na 2024.

Image
  13 Janairu, 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta  A wani kokari na tallafawa bangaren wasanni a yankunan karkara, daya daga cikin shugabannin gudanarwa na kwalejin ilimi ta tarayya dake Potiskum a jihar Yobe, Mr Nasiru Bala ja'oji ya bada gudunmuwar kudi har naira miliyan biyar ga kungiyar kwallon kafa ta Golden Boys Fc dake Kawo a jihar kaduna. Mr Nasiru Ja’oji ya bada wannan gudunmuwa ne a lokacin da yake jawabi wajen wasan karshe na gasar December cup na kawo na 2024 wanda Seyi Tinubu ya dauki nauyi. Ya bayyana cewa gasar ya samar da dama ga yan wasan domin bayyana irin baiwar da ubangiji ya musu a bangaren wasan kwallon kafa yana mai cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a shirye take wajen tallafawa matasa a wannan bangare na wasanni. Bala Ja’oji ya kuma jinjinawa shugaban shirya gasar na Seyi Tinubu wato Musa Ibrahim bisa kokarin sa na hada kan al’ummar jihar kaduna inda ya bayyana shi a matsayin Babban nasara ga jama’a. Da yake jawabi akan irin tallafin da Seyi Tin...

TA TABBATA: Hukumar La Liga ta yiwa Dani Olmo da Pau Victor Rijista.

Image
 9 ga Watan Janairun 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta. TA TABBATA: Hukumar La Liga ta tabbatar da yiwa Yan wasan Barcelona Dani Olmo da Pau Victor Rijista. A ranar Laraba ne aka amincewa Barcelona ta yiwa Dani Olmo da Pau Victor Rijista kuma Sa'oi kadan hukumar La Liga ta tabbatar da Rijistan Idan Za a iya tunawa, Hukumonin La Liga da na kwallon kafa ta kasar Spaniya sukaita yin watsi tare da kin amincewa da yiwa Olmo da Victor rijista. Wannan Labari Mai Dadi ne ga yan Barcelona kuma a yanzu Yan wasan biyu, Olmo da Victor za su iya fafata wasan karshe na Spanish Super Cup tsakaninsu da Real Madrid a ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025. Yan wasan biyu za su ci gaba da Buga Wasa har na tsawon Watanni uku Koda yake za a kara tsawaita lokacin bugawarsu har zuwa Karshen Wannan kakar Wasa idan Suka ci ga ba da yin Nasara a karar da Suka shigar.

Sabon Kocin Super Eagles, Eric Chelle zai Rika karbar naira Miliyan N85 a Matsayin Alwashinsa duk wata.

Image
 9 January, 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta. Sabon Kocin Super Tawagar Super Eagles Coach, Eric Chelle zai Rika karbar dala Dubu 55 Wanda yayi dai dai da naira Miliyan 85 da Dubu Dari tara da tamanin da hudu da Dari tara a Matsayin albashinsa duk wata. An bayyana Sunan Chelle  Matsayin Sabon Kocin Super eagles ne a ranar Talatarnan bayan non nazari da Shawarwari akan kwarewar Mai horaswar. Ana saran Sabon Kocin Kuma Tsohon Kocin kasar Mali zai iso Najeriya a ranar Asabar da mataimakansa biyu domin kaddamar dasu a ranar litinin a Birnin tarayya Abuja. A yanzu Aikin dake gaban Sabon Kocin Super eagles din shine, tunkarar Gasar Cin kofin Nahiyar Africa Masu wasu a kungiyoyin Cikin Gida wato CHAN a kasar Marocco da kuma Samun tikitin zuwa Gasar Cin kofin Duniya na 2028.

Kawo Tournadorse beat Hayin Banki to reach Seyi Tinubu kawo December Cup Final

Image
  Kawo December Cup 2024. By Usman Ibrahim Mahuta. 8 January, 2025. It was an exciting moment for thousands of spectators who witnessed the first semi-final of the Kawo Unity December Cup, sponsored by Seyi Tinubu, as Kawo Tornadoes Football Club reached the final match of the competition after defeating Hayin Banki Football Club on penalties. The game ended goalless during regulation time. However, immediately after the second half, Abdulazeez Butu, the sensational midfielder of Kawo Tornadoes, scored a brilliant goal from outside the 18-yard box. However, Hayin Banki leveled the game at 1-1 through Shafi'u Sani after receiving a good cross from their left back, Sagir Muhammad, sending the game straight to a penalty shootout. Kawo Tornadoes emerged victorious, winning 3-2. Speaking during the match, Abdul'aziz Abubakar KaKa, Chairman of the APC Stakeholders Forum, commended the organizers for their efforts, stating that the competition has proven how sports unite people irresp...

Albash FC ta Doke Zaragoza F c a Gasar Ex ministers December Cup

Image
  Gasar Ex minister December Cup Kaduna. Daga Usman Ibrahim Mahuta. kungiyar kwallon kafa ta Albash Football Academy ta Samu Nasarar zuwa wasan karshe na Gasar Ex ministers December Cup sau biyu a jere bayan data doke Zaragoza F c da ci 1-0 a wasan semi final. Wasan Daya Gudana a Talatarnan ya Samu Halartar Dandazon Yan Kallo inda Suka nishadantu da Wasannin. Bisa Wannan Nasara ne, Kungiyar kwallon kafa ta Albash Academy zata kara da Sharp shooters F c a wasan karshe domin lashe Gasar. A cewar Shugaban kwamitin Shirya Gasar, Coach Bakura Muhammad an tsara fafata wasan karshen ne idan Allah ya kaimu ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025 da yammaci a Filin wasa na Minister Unguwar Sarki Kaduna  Coach Bakura ya kuma yabawa Kungiyoyi 16 da Suka fafata Gasar bisa Gudunmuwa da Hadin kai da Suka Bada Wajen Samun Nasarar zuwa wasan karshe Lafiya inda kuma ya bukaci su dore a hakan don ci gaban Wasannin a Jihar Kaduna.

The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player.

Image
  7th January, 2025 From Usman Ibrahim Mahuta  The Story of Abdulazeez Butu (Zezu): A hardworking and talented player. Abdul'azeez Butu also known as Zezu was Born in Borno State and was brought up in kaduna State at the Nigerian Defence Academy (NDA) Barrack. He currently resides in Mahuta Community Igabi Local Government area of kaduna State, Nigeria. Abdul'azeez Butu started his Football career in the year 2009 were he played for many clubs like, Mahuta United, Rukayya Football Academy and DMF Football Academy amongst others. Abdul'azeez was born to the family of a retired Solder of the Nigerian Army where they lived in many states like, Edo, Niger, Lagos, the Federal Capital territory Abuja and his state of Origin Borno. Abdul'azeez started travelling to play outside the state when he joined Rukayya Football Academy in Kaduna State where he played for some couple of years and has travelled with the team to many places for away matches and trails for other prospectiv...

Wa nene Dan wasa Abdul'azeez Butu?

Image
  7 ga Watan Janairu, 2025 Daga Usman Ibrahim  Labarin hazikin Dan wasan tsakiya Abdul'azeez Butu. An haifi Abdul'azeez Butu ne a Jihar Borno dake Arewa ta gabashin Najeriya amma ya Girma a Barikin Soji ta NDA kuma a yanzu haka Yana zauna a Unguwar Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna a Najeriya. Abdul'azeez Butu ya Fara Buga kwallon kafa ne a shekarar 2009 inda ya buga kungiyoyi daban Daban irinsu Mahuta United da Rakiya Football Academy ya kuma Bugawa  DMF Football Academy wasu Muhinman Wasanni da dai sauransu. Abdul'azeez ya zauna a jihohi irinsu Edo da Niger da Legas da Birnin tarayya Abuja da kuma Jiharsa ta Haihuwa Borno lokacin da mahaifinsa ke Aikin Sojan Najeriya. Butu ya Fara yin tafiye tafiye ne tare da kungiyar kwallon kafa ta Rukayya Academy Kaduna inda ya kwashe wasu shekaru tare da Ita kuma Suka yi Tafiya jihohi daban Daban a Najeriya da Nufin Niman Aiki. Bugu da kari, Dan wasan tsakiyan Abdul'azeez ya Samu damar zuwa wani wasan gwajin Da...