An bukaci Teloli su Rika Cika Alkawari gabanin Azumin Watan Ramadan.
Daga Usman Ibrahim Mahuta 5 ga Watan Fabarerun 2025 An bukaci Teloli su Rika Cika Alkawari gabanin Azumin Watan Ramadan. A dai dai lokacin da Watan Azumin Ramadan ke kara kawo jiki, an Bukaci Teloli da su Rika Cika Alkawari idan an basu Dinki don biyan bukatun Al'umma. Mai Girma wakilin Mahuta Alhaji Yahuza Ibrahim ne yayi Kiran a lokacin da yake jawabi Wajen yaye dalibai Hudu da Suka Kammala koyon Aikin Dinki a garin Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna. Alhaji Yahuza Ibrahim ya ce ta Hanyar Cika Alkawari ne Sana'arsu dama kimarsu da jarajarsu zai daukaka a idan duniya yayin kuma ya ja hankalin Masu Bada Dinki su Rika biyan Telolin Hakkokinsu. A nashi jawabin, Mai Girma Sarkin Yakin Mahuta Dr Jafaru Bello Dambazau Wanda ya Samu wakilcin Malam Hussaini Mustapha ya nuna farin Cikin sa bisa Wannan Nasara da aka Samu Yana Mai Shan Alwashin bata tasa Gudunmuwar Wajen Bunkasa Sana'oi. Da yake jawabi akan Muhinmancin Sana'oi a tsakanin Matasa, Daya daga Cikin S...