Posts

Young Spiders ta lashe Gasar cin kofin Zaman Lafiya na Gwamna Uba Sani

Image
Young Spiders Kasuwan Magani ta lashe Gasar cin kofin Zaman Lafiya na Gwamna Uba Sani. Daga Usman Ibrahim  9 ga watan Ogustan, 2026. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Young Spiders ta Kasuwan Magani ta zama zakarar gasar cin kofin kwallon kafa na Gwamnan Uba Sani  da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, bayan da ta doke Kufana United da ci 2–0 a wasan ƙarshe. An gudanar da wasan ƙarshen ne a filin wasa na Kajuru Township Stadium, inda dimbin masoya ƙwallon ƙafa, shugabannin al'umma, jami'an gwamnati da sauran manyan baƙi daga ciki da wajen ƙaramar hukumar suka halarta. Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Muhammad Shuaibu, ne ya shirya gasar da nufin inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummomi daban-daban na yankin, tare da nuna goyon baya ga gwamnatin Gwamna Uba Sani.    Young Spiders ce ta fara samun damar cin ƙwallo, inda Sagiru Gambo ya buɗe ƙwallon a minti na 12, bayan da ya samu damar zura ƙwallon a raga. Ana tsaka da wasa...

Hon. Dauda Madaki ya Jaddada Aniyar Gwamnatin sa wajen Inganta tsarin Shugabanci ta hanyar anfani da Sahihan Bayanai.

Image
  HON. DAUDA MADAKI YA JADDADA ANIYAR GWAMNATINSA NA INGANTA TSARIN SHUGABANCI TA HANYAR AMFANI DA SAHIHAN BAYANAI. Daga, Usman Ibrahim Mahuta. 5 ga watan Ogustan, 2026. Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Kajuru, Honorable Dauda Madaki ya bayyana cewa gwamnatin sa zata ci gaba da barin kofarta a bude wajen gudanar da harkokin Shugabanci ga Al'umma don ci gaba. Dauda Madaki ya bayyana haka ne a cikin wata Sanarwa data samu Sanya hannun Sakataren yada labaran sa, Mr. John Ezra Sojah. Hukumar kula da kasafi da tsare-tsare ta Jihar kaduna tare da hadin gwiwar Hukumar UNICEF Ofishin kaduna ne suka shirya taron karawar Juna sanin na kwanaki Uku ga Shugabannin kananan Hukumomin Jihar kaduna a taron daya gudana a Jihar Kano. A cewar Sanarwar, Dauda Madaki ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin sa na ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Kaduna da UNICEF da sauran abokan hulɗar domin ƙarfafa ƙwarewar hukumomi, bunƙasa shugabanci mai haɗa kowa da kowa, da aiwatar da shirye-shiryen da za su...

Allah ya yiwa Sheik Shehu Usman Rigi-Rigi rasuwa

Image
2 ga Janairu, 2026 Labari daga Abubakar Dan Yaro Innalillahi wainnailaihirrajiun: Allah ya yiwa Fitacccen Malamin Addinin Musulunci nan a Jihar Kaduna, Sheik Shehu Usman Idriss wanda aka fi Sani da Regi-regi na Manzon Allah. Kafin rasuwarsa Malamin ya shahara Wajen sanya mabiyansa da Sauran Al'ummar Musulmai nishadi Saboda salon wa'azinsa. Shiek Shehu Usman ya rasu ya bar Matansa 4 da yara 37 da jikoki da dama  Za'a gudanar da Jana'izarsa da Karfe 4:30pm na yammacin yau idan Allah ya kaimu a Gidansa dake Kusfa Zaria. Da Fatan Allah ya gafarta Masa da Rahama Amin.

Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.

Image
  Yan Sanda sun ceto wasu Mutane da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi. 2 ga Janairu, 2026 Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta samu wata gagarumar nasara a yaƙin da take yi da satar mutane da fashin daji, inda ta ceto mutane biyu da aka sace tare da cafke wani wanda ake zargi, a yayin wasu aikin hadin gwiwa na magance matsalar tsaro da aka gudanar a ƙananan hukumomin Kalgo da Dandi na jihar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce aikin ya nuna ƙudirin rundunar na hana masu aikata laifuka samun mafaka a cikin jihar. Usman ya ce an ceto mutanen ba tare da sun ji rauni ba, sakamakon daukin gaggawa da jami’an tsaro da kuma kyakkyawar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Sa-kai ta Vigilante Group suka yi. Ya sake jaddada ƙudirin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi na amfani da bayanan sirri da kuma ɗaukar matakan kariya tun kafin aikata laifi, yana mai tabbatar wa al’umma cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka do...

Rundunar sojin Najeriya ta kashe mataimakin shugaban Boko Haram a Jihar Borno

Image
  Rundunar soji ta kashe mataimakin shugaban Boko Haram   2 ga Janairu, 2026 Daga Usman Ibrahim   Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe wani babban jagoran Boko Haram, wanda aka bayyana shi a matsayin mataimaki na biyu tare da wasu mayaka goma a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno. An bada rahoton cewa an kashe ‘yan ta’addan ne a yankin Komala da ke Ƙaramar Hukumar Konduga yayin wani samame da rundunar ta kai da daddare. A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sanni Uba ya fitar, ta ce an kuma kwato makamai da dama daga hannun yan ta’addan. Ya ce lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan da sojoji suka hallaka fitaccen kwamandan Boko Haram da ISWAP, Julaibib a yankin Gujba na Timbuktu Triangle. Ya ƙara da cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar da harsasai da kekuna da kayayyakin abinci da kuma magunguna masu yawan gaske. Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka. Facebook YCMC News You Tube YCMC News Tit Tok YCMC New...

Besiktas ta ki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi.

Image
  Besiktas taki amincewa da tayin Ajax na daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi. 2 ga Janairu, 2026 Daga Usman Ibrahim. kyakkyawan salon wasa da ɗan wasan tsakiya Wilfred Ndidi ya nuna a matakin kungiyarsa da ƙasarsa Najeriya ya ja hankalin ƙungiyar kwallon kafa ta Ajax dake   kasar Netherlands sai dai ƙungiyar Beşiktaş ta ƙi amincewa da tayin da aka kawo mata. Rahotanni sun nuna cewa tayin da aka tattauna ya ƙunshi aro na Yuro Miliyan Biyu ( €2m) tare da zaɓin saye na Yuro Miliyan ( €12m ) amma Beşiktaş ba ta shirya karɓar wannan tayin a wannan lokaci ba. Ndidi ya taka muhimmiyar rawa a tsakiya tare da baiwa tawagar Super Eagles gagarumin gudunmuwa a gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afirika wato AFCON na 2025 da aka kammala a kasar Morocco inda Najeriya ta kammala gasar a matsayi na uku tare da lashe lambar tagulla. Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka. Facebook YCMC News You Tube YCMC News Tit Tok YCMC News

Dan wasan Najeriya Gabriel Orok ya sanya hannu a kungiyar Al Swehli ta Kasar Libya daga Emyimba FC.

Image
  Gabriel Orok ya sanya hannu a kungiyar Al Swehli ta Kasar Libya daga Emyimba FC.   2 ga Janairu, 2026 Daga Usman Ibrahim. Dan wasan gefe na Najeriya Gabriel Orok ya kammala komawarsa dindindin zuwa ƙungiyar Al Swehli ta ƙasar Libya. Gabriel ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku da ƙungiyar ta Arewacin Afirka. Tsohon ɗan wasan Enyimba FC ya kammala sauya shekan ne bayan ya yi nasarar gwajin lafiya tare da cimma matsaya kan sharuɗɗan kwantaragin da kulob ɗin. Al Swehli ta riga ta gabatar da Orok a hukumance, tana mai tabbatar da isowarsa gabanin kakar wasa mai zuwa. Sauyin da Orok ya yi alama ce ta buɗe sabon babi a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, kasancewar wannan ne karon farko da zai taka leda a Arewacin Afirka. Ana sa ran ƙwarewarsa ta gudu, kai hari kai tsaye da iya kutsa kai za su ƙara wa sabuwar kungiyarsa Al Swehli ƙarfi a ɓangaren gefe wajen rika kai kora. Zaku Iya bibiyarmu a kafafenmu kamar haka. Facebook YCMC News You Tube YCMC News Tit...

NPFL Mako na 24, Rangers ta doke Kano Pillars, Katsina United ta doke Abia Warriors

Image
  Sakamakon wasannin gasar Kwararru ta kasa bayan kammala wasannin mako na 24. 2 ga Janairun, 2026 Daga Usman Ibrahim. Sakamakon wasannin da aka buga mako na 24 na gasar kwararru ta kasa wato (NPFL) a ranar Lahadi a filaye daban-daban. Rangers International ta doke Kano Pillars da ci  2–0  sai Katsina United ma ta samu nasara akan Abia Warriors da ci  2–0  yayin da Bayelsa United ta sha kashi da ci  1–0  a hannun Enyimba. Sauran sakamakon wasannin sun nuna cewa Wikki Tourists da Nasarawa United sun tashi canjaras wato 1–1 sai kuma Niger Tornadoes ta yi canjaras 2–2 da Bendel Insurance. Haka kuma a Litinin dinnan za’a fafata sauran wasannin mako na 24 inda El-Kanemi Warriors za ta karɓi baƙuncin Kun Khalifat sai Barau FC Kano za ta fafata da Ikorodu City a Filin Wasa na tunawa da Marigayi Sani Abacha sai Kwara United za ta kara da Warri Wolves yayin da...

MAL-MOH zai tsaya takaran Shugaban Matasan APC a Shiyyar Arewa maso Yamma

Image
  1 Janairun, 2026 Daga Usman Ibrahim Mahuta  A daidai lokacin da ake tunkarar babban taron Jam'iyyar APC na Kasa, Matasa daga Shiyyar Arewa maso Yamma na ci gaba da bayyana ra'ayin su na tsayawa takara a matakai daban daban. Na kwana kwanannan shine, Muhammad Abubakar Mal-moh Wanda ya bayyana aniyarsa na tsayawa takaran Shugaban Matasa na Jam'iyyar APC a Shiyyar Arewa maso Yamma. Taron ya gudana ne Jihar Kaduna inda magoya bayan Muhammad Abubakar Mal-Moh suka  taru domin shaida ayyana kudirinsa na tsayawa takarar Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma, gabanin babban taron kasa na jam’iyyar da ke tafe. Da yake bayyana kudirinsa, Muhammad Abubakar Mal-Moh ya ce shawarar da ya yanke ta biyo bayan tuntuba mai zurfi da ga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a matakin jiha da na kasa, musamman matasa. Ya bayyana cewa Shirin MAL-MOH an kirkire shi ne domin tallafawa kokarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani wajen kar...

MAL-MOH Unveils Ambition for APC North-West Youth Leader Seat

Image
Usman Ibrahim Mahuta  1 January, 2026  As preparations intensify ahead of the All Progressives Congress (APC) National Convention, youths across the North-West zone have continued to express interest in contesting for key leadership positions within the party. One of such aspirants is Muhammad Abubakar Mal-Moh, who has officially declared his intention to vie for the position of APC Zonal Youth Leader, North-West, under a project tagged “MAL-MOH Project.” Declaring his ambition, Muhammad Abubakar Mal-Moh said his decision followed wide consultations with key stakeholders of the party at both state and national levels, with particular emphasis on the youth. He explained that the MAL-MOH Project is designed to complement the efforts of President Bola Ahmed Tinubu and Kaduna State Governor, Senator Uba Sani in empowering young people, while also strengthening the APC’s grassroots support across the North-West zone. Speaking at the event, the Senior Special Assistant to the Kaduna...

Kaduna Polytechnic tayi cikakken bayani akan jinkirin Kiran dalibai da suka Kammala karatu zuwa aikin yiwa Kasa hidima.

Image
  Daga Auwal Ahmed Ibrahim, Goronyo. 31 ga Janairu 2026 Hukumar Gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya dake Jihar Kaduna (Kadpoly) ta fitar da sanarwa domin amsa korafe-korafen da wasu daliban da suka kammala karatu ke yi game da jinkirin kiran su aikin bautar ƙasa ta NYSC. Hukumar ta bayyana cewa wannan jinkiri ba na Kadpoly kaɗai ba ne, illa ya shafi dukkan manyan makarantu a faɗin ƙasar nan, musamman waɗanda ke da yawan ɗaliban da suka kammala karatu, sakamakon yawan tantance bayanai da matakan da ake bi. A cikin Sanarwa ta Musamman da Magatakardar Kwalejin, Dr. Muhammad Tanimu, ya rubuta kuma ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa manyan abubuwan da ke haddasa jinkirin sun haɗa da rashin yin daidaitaccen regularization da Hukumar Shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Ƙasa JAMB), kura-kurai ko rashin cika takardun da ake buƙata daga ɓangaren waɗanda suka kammala karatu, da kuma tsarin rukunnan dalibai wato batch da NYSC ke amfani da shi. Magatakardar ya ƙara da cewa an...

An bukaci Teloli su Rika Cika Alkawari gabanin Azumin Watan Ramadan.

Image
 Daga Usman Ibrahim Mahuta  5 ga Watan Fabarerun 2025 An bukaci Teloli su Rika Cika Alkawari gabanin Azumin Watan Ramadan. A dai dai lokacin da Watan Azumin Ramadan ke kara kawo jiki, an Bukaci Teloli da su Rika Cika Alkawari idan an basu Dinki don biyan bukatun Al'umma. Mai Girma wakilin Mahuta Alhaji Yahuza Ibrahim ne yayi Kiran a lokacin da yake jawabi Wajen yaye dalibai Hudu da Suka Kammala koyon Aikin Dinki a garin Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna. Alhaji Yahuza Ibrahim ya ce ta Hanyar Cika Alkawari ne Sana'arsu dama kimarsu da jarajarsu zai daukaka a idan duniya yayin kuma ya ja hankalin Masu Bada Dinki su Rika biyan Telolin Hakkokinsu. A nashi jawabin, Mai Girma Sarkin Yakin Mahuta Dr Jafaru Bello Dambazau Wanda ya Samu wakilcin Malam Hussaini Mustapha ya nuna farin Cikin sa bisa Wannan Nasara da aka Samu Yana Mai Shan Alwashin bata tasa Gudunmuwar Wajen Bunkasa Sana'oi. Da yake jawabi akan Muhinmancin Sana'oi a tsakanin Matasa, Daya daga Cikin S...

Wakilin Sarkin Zuru ya Bukaci Samar da Cibiyoyin koyon Sana'oi

Image
 Daga Usman Ibrahim Mahuta  3 ga Watan Fabarerun 2025. An bukaci a samar da Karin Cibiyoyin koyon Sana'oi a Cikin Al'umma. Mai Girma wakilin Sarkin Zuru na Jihar Kaduna, Engineer Zubairu Kabir Danjuma ya bukaci Shugabannin da Sauran Masu Hannu da shuni su samar da Cibiyoyin koyon Sana'oi ga Matasa domin rage yawan zaman kashe Wando  Cikin Al'umma. Engineer Zubairu Kabir Danjuma ya bukaci hakan ne a lokacin da yake jawabi Wajen yaye dalibai Hudu da Suka Kammala koyon Aikin Dinki a garin Mahuta dake Karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna Wanda kungiyar Teloli na Mahuta ta shirya . Mai Girma wakilin Sarkin Zuru, ya bayyana Cewa matukar aka samar da Wuraren koyon Sana'oi zai taimaka ba kadanba domin kuwa Mata da Matasa zasu Samu aikinyi. Engineer Zubairu Kabir ya kuma shawarci Matasa da su kaucewa jiran Aikin Gwamnati a maimakon haka su Rungumi Sana'oin hannu domin shine kadai Hanya mafita Wanda zai su rike kansu. Ya Kuma jinjinawa kungiyar Teloli na Mahuta karkashin...

Northwell Academy ta Lashe Gasar W/ Sarkin Zuru December Cup U14 Mahuta sau biyu a Jere

Image
 25 ga Watan Janairun 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta. Kungiyar kwallon kafa ta Northwell Football Academy Makera dake Karamar hukumar Kaduna ta Kudu ta lashe Gasar December Cup Wanda Wakilin Sarkin Zuru na Jihar Kaduna Injiniya Zubairu Kabir Danjuma ya Shiryawa Matasa Yan Kasa da shekaru 14 a Mahuta. Northwell ta doke kungiyar kwallon kafa ta Lion Stars Football Club ne. da ci 3-2 a wasan karshe da Suka Buga a Asabar Dinnan kuma ya lashe Gasar sau biyu a jere kenan. Idan za a iya tunawa, a shekarar 2024 Northwell ce ta Doke Kungiyar kwallon kafa ta Athletic Academy a wasan karshe kuma ta Lashe Gasar. Dan wasan tsakiya Abdullatif Tajudeen shine ya lashe kyautar mafi kwazo a Kananan Yara sai Simon Friday ya lashe kyautar Wanda ya fi kowa Zura kwallo da guda hudu yayin da aka baiwa Daukacin kungiyoyin da Suka fafata a Gasar takardar Shaidar fafatawa a Gasar. Mai Girma wakilin Sarkin Zuru ya nuna Farin Cikin sa bisa irin Yan wasan Daya ganewa idanunsa Yana Mai jaddada muhinmancin wasan...

Golden Boys kawo ta Lashe Seyi Tinubu Kawo December Cup 2024 bayan Doke Tornadoes

Image
 13 Janairu, 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta  Kungiyar kwallon kafa ta Golden Boys Fc dake Kawo Kaduna ta lashe gasar cin kofin zaman lafiya wanda Seyi Tinubu ya dauki nauyi na Kawo December Cup bayan data doke Kawo Tornadoes da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaran raga a wasan karshen. Golden Boys ce ta fara zura kwallo jim kadan da fara wasan amma kafin aje hutun rabin lokacin Abdulazeez Butu na Kawo Tornadoes mai maida wasan 1-1 a a Zangon farko na wasan bayan da suka samu finareti inda daga nan ne aka je bugun daga kai sai mai tsaran raga. Yan wasan Tornadoes biyu sun barar da kwallo biyu wanda hakan ya baiwa Golden Boys lashe gasar. Da yake jawabi a lokacin wasan, Babban mai baiwa shugaban kasa Tinubu shawara akan hulda da al’umma a yankin arewa maso gabas,, Abdulhameed Yahaya Abba ya yabawa Seyi Tinubu da kwamitin shirya gasar bisa kokarin su inda ya kara da cewa sannu a hankali gasar na dawo da martabar kwallon kafa a jihar kaduna. Suma a jawabin su, shugaban karamar h...

Hon. Nasiru Ja’oji ya baiwa Golden Boys kawo Miliyan 5 bayan lashe gasar Seyi Tinubu kawo December Cup na 2024.

Image
  13 Janairu, 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta  A wani kokari na tallafawa bangaren wasanni a yankunan karkara, daya daga cikin shugabannin gudanarwa na kwalejin ilimi ta tarayya dake Potiskum a jihar Yobe, Mr Nasiru Bala ja'oji ya bada gudunmuwar kudi har naira miliyan biyar ga kungiyar kwallon kafa ta Golden Boys Fc dake Kawo a jihar kaduna. Mr Nasiru Ja’oji ya bada wannan gudunmuwa ne a lokacin da yake jawabi wajen wasan karshe na gasar December cup na kawo na 2024 wanda Seyi Tinubu ya dauki nauyi. Ya bayyana cewa gasar ya samar da dama ga yan wasan domin bayyana irin baiwar da ubangiji ya musu a bangaren wasan kwallon kafa yana mai cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a shirye take wajen tallafawa matasa a wannan bangare na wasanni. Bala Ja’oji ya kuma jinjinawa shugaban shirya gasar na Seyi Tinubu wato Musa Ibrahim bisa kokarin sa na hada kan al’ummar jihar kaduna inda ya bayyana shi a matsayin Babban nasara ga jama’a. Da yake jawabi akan irin tallafin da Seyi Tin...

TA TABBATA: Hukumar La Liga ta yiwa Dani Olmo da Pau Victor Rijista.

Image
 9 ga Watan Janairun 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta. TA TABBATA: Hukumar La Liga ta tabbatar da yiwa Yan wasan Barcelona Dani Olmo da Pau Victor Rijista. A ranar Laraba ne aka amincewa Barcelona ta yiwa Dani Olmo da Pau Victor Rijista kuma Sa'oi kadan hukumar La Liga ta tabbatar da Rijistan Idan Za a iya tunawa, Hukumonin La Liga da na kwallon kafa ta kasar Spaniya sukaita yin watsi tare da kin amincewa da yiwa Olmo da Victor rijista. Wannan Labari Mai Dadi ne ga yan Barcelona kuma a yanzu Yan wasan biyu, Olmo da Victor za su iya fafata wasan karshe na Spanish Super Cup tsakaninsu da Real Madrid a ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025. Yan wasan biyu za su ci gaba da Buga Wasa har na tsawon Watanni uku Koda yake za a kara tsawaita lokacin bugawarsu har zuwa Karshen Wannan kakar Wasa idan Suka ci ga ba da yin Nasara a karar da Suka shigar.

Sabon Kocin Super Eagles, Eric Chelle zai Rika karbar naira Miliyan N85 a Matsayin Alwashinsa duk wata.

Image
 9 January, 2025 Daga Usman Ibrahim Mahuta. Sabon Kocin Super Tawagar Super Eagles Coach, Eric Chelle zai Rika karbar dala Dubu 55 Wanda yayi dai dai da naira Miliyan 85 da Dubu Dari tara da tamanin da hudu da Dari tara a Matsayin albashinsa duk wata. An bayyana Sunan Chelle  Matsayin Sabon Kocin Super eagles ne a ranar Talatarnan bayan non nazari da Shawarwari akan kwarewar Mai horaswar. Ana saran Sabon Kocin Kuma Tsohon Kocin kasar Mali zai iso Najeriya a ranar Asabar da mataimakansa biyu domin kaddamar dasu a ranar litinin a Birnin tarayya Abuja. A yanzu Aikin dake gaban Sabon Kocin Super eagles din shine, tunkarar Gasar Cin kofin Nahiyar Africa Masu wasu a kungiyoyin Cikin Gida wato CHAN a kasar Marocco da kuma Samun tikitin zuwa Gasar Cin kofin Duniya na 2028.

Kawo Tournadorse beat Hayin Banki to reach Seyi Tinubu kawo December Cup Final

Image
  Kawo December Cup 2024. By Usman Ibrahim Mahuta. 8 January, 2025. It was an exciting moment for thousands of spectators who witnessed the first semi-final of the Kawo Unity December Cup, sponsored by Seyi Tinubu, as Kawo Tornadoes Football Club reached the final match of the competition after defeating Hayin Banki Football Club on penalties. The game ended goalless during regulation time. However, immediately after the second half, Abdulazeez Butu, the sensational midfielder of Kawo Tornadoes, scored a brilliant goal from outside the 18-yard box. However, Hayin Banki leveled the game at 1-1 through Shafi'u Sani after receiving a good cross from their left back, Sagir Muhammad, sending the game straight to a penalty shootout. Kawo Tornadoes emerged victorious, winning 3-2. Speaking during the match, Abdul'aziz Abubakar KaKa, Chairman of the APC Stakeholders Forum, commended the organizers for their efforts, stating that the competition has proven how sports unite people irresp...

Albash FC ta Doke Zaragoza F c a Gasar Ex ministers December Cup

Image
  Gasar Ex minister December Cup Kaduna. Daga Usman Ibrahim Mahuta. kungiyar kwallon kafa ta Albash Football Academy ta Samu Nasarar zuwa wasan karshe na Gasar Ex ministers December Cup sau biyu a jere bayan data doke Zaragoza F c da ci 1-0 a wasan semi final. Wasan Daya Gudana a Talatarnan ya Samu Halartar Dandazon Yan Kallo inda Suka nishadantu da Wasannin. Bisa Wannan Nasara ne, Kungiyar kwallon kafa ta Albash Academy zata kara da Sharp shooters F c a wasan karshe domin lashe Gasar. A cewar Shugaban kwamitin Shirya Gasar, Coach Bakura Muhammad an tsara fafata wasan karshen ne idan Allah ya kaimu ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025 da yammaci a Filin wasa na Minister Unguwar Sarki Kaduna  Coach Bakura ya kuma yabawa Kungiyoyi 16 da Suka fafata Gasar bisa Gudunmuwa da Hadin kai da Suka Bada Wajen Samun Nasarar zuwa wasan karshe Lafiya inda kuma ya bukaci su dore a hakan don ci gaban Wasannin a Jihar Kaduna.